1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus: 29.05.2020

Usman Shehu Usman GAT
May 29, 2020

Jaridun Jamus na wannan mako sun duba shirin yin sulhu a Mali, da zaben sabon shugaban kasa a Burundi, da fadan makiyaya a Sudan ta Kudu da almundahana da tallafin Coronavirus a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/3czGl
Burundi Präsidentschaftswahl Evariste Ndayishimiye
Hoto: Reuters/E. Ngendakumana

1. Die Tageszeitung: Yinkurin yin sulhu a kasar Mali

A daukacin kasar Mali yanzu a shirye muke mu yi sulhu a yafe wa juna. wannan shi ne kalaman shugaban hukumar sasanta 'yan kasa Ousmane Sidibé ya bayyana. Wannan shi ne sharhin da za mu fara a cikin jaridun namu. Wannan Labarin jaridar Die Tageszeitung ce ta ruwaito shi, inda jaridar ta ci gaba da cewa. Shugaban hukumar sasanta al'ummar ta Mali ya ce babban abin da za su fara sawa a gaba shi ne gano mutannen da suka ji rauni, a gano wadanda dukkan rikicin ya shafa sai kuma komai ya biyo baya.  Tageszeitung ta ci gaba da cewa, a kasar Mali da rikicin ya yi wa illa, akwai bangarori da yawa dauke da makamai kuma an take hakkin dan Adam a bangarori masu yawa, wannan kuwa abu ne da ke matukar bukatar zaman a fahimci juna a yafe wa juna a cewar Ousmane Sidibé da jaridar ta yi hira da shi. Wanda kuma shi ne babban dalilin kafa hukumar jin bahasi da sasanta jama'a. 

Mali Bamako | Einsturz eines dreistöckigen Gebäudes
Hoto: DW/P. Lorgerie

 

2. Neues Deutschland: Dan takarar adawa ya ci zaben shugaban kasa a Burundi
Ita kuwa jaridar Neues Deutschland, ta yi sharhinta ne a kan sabon shugaban kasar Burundi, jaridar na mai cewa, bayan takaddamar da ta mamaye siyasar Burundi, a yanzu dai ta tabbata Janar Evariste Ndayishimiye mai ritaya, shi ne zai gaji Pierre Nkurunziza, wanda sanadiyar mallakewar mulkin da ya yi, lamarin ya jefa Burundi cikin tashin hankali. Sai dai a yanzu ma 'yan adawa sun daura damarar yin fito na fito da sabuwar gwamnati. Tun gabanin fitar da sakamakon zabe, sojoji da 'yan sanda suka bazama cikin manyan biranen kasar, bayan da 'yan adawa suka hau kan titi suna boren kin amincewa da sakamkamkon zaben. 'Yan sandan dai suk kama akalla mutane 150 daga bangaren 'yan adawa, inda gwamnati ke kokarin hana duk wata tarzoma barkewa, yayin da a gefe guda take son tabbatar da dan takarar gwamnati  Evariste Ndayishimiye ya zama shugaban kasa.

 

3. Frankfurter Allgemeine Zeitung: Rikicin makiyaya a Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu fadace-fadace tsakanin makiyaya sai kara kazanta suke yi, wannan shi ne sharhin Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ce, duk da cewa an dan samu lafawar tashin hankali tsakanin gwamnati da 'yan tawaye, amma kuma a Jihar Jonglei, kwanakin nan an samun fadan kabilanci tsakanin kabilun Maurle da Lou-Nuer. Akallla kauyuka 28 a yanzu rikicin ya ritsa da su, inda akalla aka kashe mutane 658, aka jikkata 452, yayin da kuma aka sace wasu mutane kimanin 592. Wannan kuwa duk ya faru ne watanni uku farkon bana, inda jaridar ta kara da cewa kawo yanzu dubban mutane suka tsere daga gidajensu, abin da ke nuna alamar samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu sai a hankali.

Südsudan - Freilassung von Kindersoldaten
Hoto: Getty Images/AFP/S. Glinski

 

4. Süddeutsche Zeitung: Almundahana da tallafin Corona a Afirka ta Kudu

Sai kuma yanzu mu tsallaka zuwa kasar Afirka ta Kudu, inda jaridar Süddeutsche Zeitung, ta bayyanan cewa ba taimakon juna kuma babu tausaya wa na kasa. Jaridar ta ci gaba da cewa a kasar Afirka ta Kudu tun shekaru ake ta kokoken yaduwar cin hanci da rashawa. To ko da wannan lokacin annobar Coronavirus, kayayyakin tallafi ba sa isa hannun mabukata wadanda ake bayar da taimakon dominsu. Jaridar ta ce maimakon a yi ta samun labarin mutanen da suka amfana da irin tallafin da ake bayarwa, amma kawai sai aka yi ta bude kamfanoni masu zaman kansu da sunan raba agajin COVID-19 ga mabukata, abin da kuma ya yi sanadin wawure kayakin agaji.