1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala AMA
September 25, 2020

Batun rantsar da tsohon ministan tsaro Mali Bah Ba N'Daou a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi a Mali da batun 'yan gudun hijirar Afirka masu neman mafaka a Turai sun ja hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3j0l8
Ausschnitt | Mali Bamako | Jean-Ayves Le Drian und Bah N'Daw
Bah N'Daw sabon shugaban gwamnatin wucin gadi a MaliHoto: Habibou Kouyate/AFP/Getty Images

Za mu fara da Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung da kuma Die Tages Zeitung wadanda suka rubuta sharhinsu a kan kasar Mali tare da yin waiwaye kan halin da ake ciki a kasar Mali wata guda bayan juyin mulkin sojin daya hambarar da gwamnatin Imbrahim Boubacar Keita. Jaridar ta ce rantsar da tsohon ministan tsaro Bah Ba N'Daou a wannan juma'ar a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi da kuma Assimi Goita a mukamin mataimakin shugaban kasa ya sanya dan ba na komawar kasar ta yammacin Afirka kan turbar dimukuradiyya. Gabanin wannan lokaci dai tsawon makonni yan adawa da wakilan kungiyar raya cigaban kasashen yammacin Afirka ECOWAS sun yi ta muhawara kan yadda za a ciyar da kasar gaba wadda ke da yawan al'umma miliyan 20.

Kungiyar ta ECOWAS mai mambobin kasashe ta sanya wa kasar takunkumi tare da rufe iyakokinta da kasar Mali. Sai dai kuma jaridar ta ce ko da yake ECOWAS din ta yi maraba da bin sharadinta da mahukuntan sojin suka yi. Abin jira shi ne lokacin da ECOWAS din za ta dage wa kasar takunkumin. Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo wanda ke rike da shugabancin karba karba na kungiyar yace suna sa ido tare da bi sau da kafa yadda al'amura ke gudana a Malin. A hannu guda kungiyoyin agaji na gargadi game da aukuwar fari a kasar yayin da dubban jama'a suka kaurace wa yankin saboda ayyukan yan ta'adda. Bugu da kari Jaridar ta ce matsalolin tattalin arziki da annobar Corona da kuma ambaliyar ruwa sun kara tagaiyara rayuwar al'umma a kasar inji jaridar Die Tages Zeitung. 

'Yan gudun hijirar Afirka na neman mafaka A sharhinta mai taken Afirka ta yi shiru kan kwaskwarima ga dokokin kungiyar tarayyar Turai na karbar yan gudun hijira. Sabuwar manufar kungiyar tarayyar Turai kan yan gudun hijira zai tsaurara matakan mayar da yan gudun hijira zuwa kasashen da suka fito. Jaridar tace sabbin manufofin da hukumar tarayyar Turai ta gabatar a ranar Larabar da ta gabata za su tsaurara matakai mafi tsauri da kungiyar ta dauka a tsawon tarihi. Jaridar tace wani zai yi tsammanin matakin zai jawo martani daga kasa kamar Najeriya, daya daga cikin kasashen da aka fi samun kwararar yan gudun hijira zuwa turai a yan shekarun bayan bayan nan, musamman kasancewar yawancin yan Najeriyar da suka cike takardun neman mafakar siyasa an yi watsi da bukatunsu.

Ursula von der Leyen's Rede zur Lage der EU
Ursula Von Der Leyen shugabar hukukumar gudanarwa ta EUHoto: AFP/J. Thys

To amma babu abinda aka ji ko aka gani a shafukan Internet na manyan jaridun kasar mafi yawan al'umma a Afirka da ke da mutane fiye da miliyan 200. Hakazalika Jaridar ta ce babu wani martani da aka gani ko da a shafukan Twitter na ministocin gwamnatin. Haka ma dai lamarin yake ga sauran kasashen na Afirka. A shekarar da ta gabata kasashe takwas na Afirka na daga cikin kasashe 20 da mutanensu suka fi kwarara zuwa cikin kasashen kungiyar tarayyar Turai. Kuma saboda annobar Corona da yawan haihuwa akwai alamun lamarin na iya yin kamari a nan gaba.

Ba kasafai ake maganar 'yan gudun hijira ba a NajeriyaBatun yan gudun hijira yana taka muhimmiyar rawa wajen muhawara a fagen siyasa a Turai. Sai dai a Najeriya ba kasafai akan ji hakan ba. Hasali ma sai dai batun cewa ya kamata tarayyar Turai ta cika alkawuran da ta yi musu na gudunmawa domin yaki da matsalolin da suke haddasa gudun hijira. Jaridar ta ce ko da yace wannan abu ne da zai amfani ita kanta nahiyar Turai, idan aka sami kyautatuwar rayuwar al'umma a Afirka. Idan hakan ta samu to kuwa batun da ake magana akansa na mayar da yan gudun hijira kasashensu na asali, lamarin zai bunkasa.

Marokko Oujda Illegale Migranten aus Mali
Bakin haure 'yan Afirka masu hankorin zuwa TuraiHoto: Abdelhak Senna/AFP/Getty Images

Jaridar ta Die Welta tace dalilin da ya sa ba a jin batun yan gudun hijira a siyasar Najeriya da ma rashin nuna sha'awa a kan batun shi ne kamar yadda wani jami'i na cibiyar Konrad Adenauer a Najeriya ya nunar, yan siyasar na ganin wannan matsala ce ta kasashen Turai amma ba ta Najeriya ba. A saboda haka maimakon raguwa za a cigaba da samun karuwar yan gudun hijra ne na Najeriya zuwa kasashen Turai.