1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haddura a karshen shekara a Afirka

Zakari Sadou LMJ
December 29, 2020

Hadari a kasashen Afirka da dama musamman a lokutan bukukuwan ko kuma watannin hudu na karshen shekara na zaman ruwan dare.

https://p.dw.com/p/3nKHs
Verkehrsunfälle Angola
Daukar fasinjoji da kayan da suka wuce kima, na zaman guda daga cikin abubuwan da ke janyo haddura a AfirkaHoto: Pedro Borralho Ndomba

A kasar Kamaru ga misali, cikin watanni ukun karshen 2020 alkaluman hukumar kiyaye afkuwar hadura a kasar sun nunar da cewa mutane 571 ne suka rasa rayukansu tsakanin watan Satumba zuwa Disamba. Nazari kan haddura a kasar na cewa hakan zai ci gaba da faruwa, idan dai mahukunta ba su dauki mataki ba. Hadduran dai sun fi tsananta ne a tsakanin hanyoyin Douala da Bafoussam da Yaounde da Bafoussam sai kuma a jihar Adamawar kasar, da ake alakantawa da rashin hanyoyi masu kyau ko kuma tukin ganganci.

A karshen makon jiya dai kimanin mutane 40 ne suka rasa rayukansu bayan da wata mota kirar bus mai daukar fasinjoji 70 da ta taso daga Bafoussam zuwa babban birnin kasar Yaounde, ta fada cikin rami. Hakan dai ya afku ne a kokarin da direbanta ke yi na kaucewa wata mota, inda mutane da dama suka jikkata. Rashin bin ka'idoji da aka sanya na daga cikin abubuwan da ke haddasa karuwar haddura a fadin kasar ta Kamaru, idan aka yi la'akari da yadda direbobi a wannan lokaci ke gudu da matoci ba tare da mutunta matakai ba.

Symbolbild | Unfall in Kamerun | Knapp 40 Tote
Jami'an tsaro na korafi kan rashin bin ka'idojin tukiHoto: Joel Kouam/AP Photo/picture alliance

Wannan abu dai na ciwa sojoji masu sanya ido kan harkokin tsaro a hanyoyin Kamaru tuwo a kwarya. Laftanar Kanal Olivier Ekani mai kula da harkokin tsaron na zirga-zirgar ababen hawa tsakanin Yaounde da Ebolowa ya ce: "Muna samun mutane masu yawan gudu, ya kamata ai musu bayani, kuma da akwai matsalar daura bel a kujerun motoci da rashin bin layin da aka zayyana."

Yawan mace-mace a kan hanyoyin Kamaru ya ragu zuwa 937 kwatankwacin kaso 48 cikin 100 a shekara ta 2019, kamar yadda ministan sufuri Jean Ernest Massena Ngalle Bibehe ya nunar. Rahoton Hukuma Kula da Haddura ta Kamaru, ya nunar da cewa karya dokar gudu ce tafi haddasa afkuwar hadduran da suka kai 502, sama da kaso 49 cikin 100 ke nan, na abubuwan da ke haddasa hadari. Kasar Kamaru tana rijistar kimanin sama da haddura a hanyoyi 1,600 a kowace shekara, wanda kuma ke yin sanadiyyar asarar rayukan sama da mutane 1,200 bisa kididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ko OMS.