1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afkawa gangamin adawa a Kwango

Yusuf BalaSeptember 16, 2015

Wannan dai na zama gangami da ya sami halartar 'yan adawa da dama tun bayan na watan Janairu da a lokacinsa mutane 40 suka rasu bayan gwabzawa da jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/1GX8B
Demokratische Republik Kongo Wahl Wahlen 2011 Kinshasa Opposition
'Yan adawa a Jamhuriyar Dimokradiyar KwangoHoto: AP

A kalla wasu mutane uku ne suka samu raunika bayan da wasu mutane dauke da duwatsu da kulake da itatuwa suka afkawa gangamin 'yan adawa a birnin Kinshasa na kasar Kwango wadanda ke neman shugaba Joseph Kabila ya sauka daga mukaminsa da zarar wa'adin mulkinsa ya cika a shekara mai zuwa.Vital Kamerhe shi ne jagoran na 'yan adawa.

Ya ce" Da fari na yi Allah wadai kan wannan farmaki , saboda mun mutunta doka mun sabnar da mahukunta cewa zamu yi wannan gangami a wannan rana da wannan lokaci , wannan ne ma ya sa 'yan jarida suka zo dan su sheda kuma kunga abin da ya faru, wannan ya sabawa ka'ida".

A bangaren gwanmnatin kasar kuwa ya ce zai yi bincike dan gano wadanda suka aikata wannan farmaki kan gangamin na adawa.

Wannan dai na zama gangami da ya sami halartar 'yan adawa da dama tun bayan na watan Janairu da dubban mutane suka fito dan nuna adawa da shirin shugaba Kabila na neman gyara kundin tsarin mulkin kasar, inda mutane 40 suka rasa ransu bayan da jami'an tsaro suka afkawa masu zanga-zanga.