1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

May 4, 2007

Har yau zaben Nijeriya na ci gaba da daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPH

A wannan makon ma dai jaridun na Jamus sun ci gaba da bitar halin da ake ciki a Nijeriya sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi makon da ya wuce, kazalika da hali da ake ciki a Somaliya da kuma lardin Darfur. Daga cikin jaridun da suka tabo matsalar ta Nijeriya har da jaridar Die Tageszeitung ‘yar Berlin, wadda take cewa:

“Wani abin mamaki dangane da zhaben Nijeriya da ake zargin magudi da zamba da kuma zalunci a sakamakonsa, wanda kuma akan haka ne ‘yan hamayya a karkashin jagorancin dan takara Muhammed Buhari suka kuduri niyyar yin amfani da ranar daya ga watan mayu domin zanga-zangar adawa da zaben, amma sai ga shi ba zato ba tsammani kungiyar nan dfa tayi kaurin suna mai kiran kanta kungiyar neman ci gaban yankin Nigerdelta ta Mend a takaice ta fito fili tana mai bayyana goyan bayanta ga jam’iyyar PDP tana mai barazanar bayyana ballewar yankin na Nigerdelta idan har an kuskura aka soke sakamakon zaben aka kuma nemi gudanar da wani sabon zabe.”

Ko da yake a karshen makon da ya gabata an samu ‘yar sararawar al’amura a Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya, amma bangarori da dama na kasar ana fama da dubban daruruwar ‘yan gudun hijira da suka tagayyara, a yayinda gwamnatin wuci gadi ta kasar dake hana ruwa gudu wajen gabatar musu da taimako, kamar yadda jaridar Frankfurter Rundschau ta nunar ta kuma kara da cewar:

Wani mummunan ci gaba a game da rikicin na kasar Somaliya shi ne kame-kame na ba gaira ba dalili da ake wa ‘yan gudun hijirar. Galibi ma ko da tabo ne dan kankane aka gano a hannun mutum sai a tuhumance shi da zama dan ta’adda. A dai halin da ake ciki yanzu wahalar ta ‘yan gudun hijirar Somaliyar ita ce mafi muni a duk fadin duniya.

A karo na farko kotun kasa da kasa akan miyagun laifuka ta nema da a gabatar da umarnin tsare jami’in gwamnatin wata kasa dangane da ta’asar rikicin Darfur. Jaridar Die Tageszeitung tayi bitar wannan ci gaba tana mai cewar:

A karo na farko tun bayan kafa ta a shekara ta 2002 kotun kasa da kasa akan miyagun laifuka dake birnin The Hague ta ba da umarnin cafke wani jami’i na gwamnati, inda a wannan makon ta gabatar da umarnin cafke wani minista na gwamnatin Sudan da kuma wani shugaban dakarun sa kai, wadanda ake dora musu alhakin ta’asar yakin lardin Darfur. Wannan maganar ta shafi Ahmed Haroun ne, wanda ke da alhakin al’amuran Darfur a ma’aikatar cikin gida ta Sudan daga shekara ta 2003b zuwa ta 2004, da kuma Ali Kushyb daya daga cikin shuagabannin dakarun larabawan Janjaweed wadanda kowane daga cikinsu ake zarginsa da laifuka kusan hamsin da suka shafi cin zarafin dan-Adam a lardin Darfur.

Ita kuwa jaridar Die Zeit ta leka ne kasar Zimbabwe domin sake bitar halin da ake ciki a wannan kasa, inda ta gano cewar a dai halin da ake ciki yanzun Zimbabwe na da yawan marasa aikin yi kimanin kashi 70% na illahirin al’umarta a yayinda take fama da hauhawar farashin kaya ta kashi 1700%. Kasar kazalika tana fama da karancin kayan masarufi na yau da kullum da kuma tsadar fetur a magunguna. Jaridar ta ce kusan dai a ce kome ya tsaya ne cik babu wani abin dake motsi a kasar.