1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

June 23, 2006

Maganar shari'ar Charles Taylor a The Hague na daya daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin Jamus

https://p.dw.com/p/BvPq
Charles Taylor
Charles TaylorHoto: AP

Maganar shari’ar tsofon shugaban kasar Liberiya Charles Taylor, wanda a yanzu aka tasa keyarsa zuwa The Hague ta kasar Netherlands domin gabatar da shi gaban kuliya akan zarginsa da kashe-kashe na gilla da ta’asar yaki da kuma wawason baitul-malin kasar Liberiya. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

„Tun bayan cafke shi da aka yi a lokacin da yake kokarin rantawa a na kare a wajejen karshen watan maris da ya wuce aka gabatar da Taylor gaban kotu, amma aka gano cewar za a fuskanci matsaloli ta fuskar tsaron lafiyarsa a Freetown. A baya ga haka akwai fargabar makomar zaman lafiyar kasar Saliyo da ta sha fama da yakin basasa. A sakamakon haka kasar Netherlands ta ce a shirye take ta amince da a ci gaba da shari’ar a kotun kasa da kasa dake The Hague, a yayinda ita kuma Birtaniya ta ce a shirye take ta tsare shi a gidan kurkuku bayan an yanke masa hukunci.“

Har yau ana fama da mawuyacin hali na zaman dardar a lardin Darfur na yammacin kasar Sudan duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma game da yankin a wasu ‚yan makonnin da suka wuce, in ji jaridar NEUES DEUTSCHLAND wadda ta kara da cewar:

„Ba dukkan kungiyoyin tawaye dake da hannu a rikicin suka amince da yarjejeniyar zaman lafiyar lardin Darfur ba a sakamakon haka ake gaba da fama da fada tsakanin kungiyoyin dake cikin damar makamai da kuma kai farmaki kann farar hula. A hakika ma dai babu wani sauyin da aka samu a game da mawuyacin halin da ake ciki a sansanonin ‚yan gudun hijira, wadanda ba zasu iya komawa gidajensu ba sakamakon rashin tsaro.“

A daidai lokacin da ake shirye-shiryen tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen kungiyar tarayyar Turai zuwa janhuriyar demokradiyyar Kongo sai ga wata sabuwar tabargaza ta billo, inda ake tuhumar wasu sojan kiyaye zaman lafiya na MDD da laifuka na kisan kai. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

„Gidan telebijin Birtaniya na Channel Four shi ne ya fallasa wannan tabargaza a cikin wani shirin rahotannin da yake da niyyar gabatarwa a yau juma’a. Bayanin da telebijin din ya bayar yana mai yin nuni ne da wasu sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD daga kasashen Afurka ta Kudu da Pakistan, wadanda suka rufa wa sojan gwamnati baya a wani matakin faramaki da suka dauka kann wasu dakarun sa kai a lardin Ituri a karshen watan afrilun da ya wuce. A wannan mataki sojojin na MDD da takwarorinsu na janhuriyar demokradiyyar kongo sun yi kaca-kaca da wani kauye da ake kira Kazana dake lardin. MDDr ta yi alkawarin bin bahasin lamarin. Tun kuwa da jimawa ake zargin hadin kai da sojan MDD ke ba wa sojan kasar Kongo domin murkushe dakarun sa kai a gabacin kasar.“