1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

January 7, 2005

Halin da ake ciki a kasar Sudan na daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon mai karewa

https://p.dw.com/p/BvpY

A wannan makon, ko da yake hankali ya fi karkata ga mawuyacin halin da ake ciki a yankunan da masifar ambaliyar teku ta tsunami ta rutsa da su a kudu da kuma kudu-maso-gabacin Asiya, amma duk da haka jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni iya gwargwado akan al’amuran Afurka. Amma tun da yake mun tabo maganar tsautsayin na tsunami zamu fara da sharhin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta a game da tasirin hada-hadar taimakon kasashen na Asiya da bala’in ya shafa akan manufofin taimakon raya sauran kasashe masu tasowa, musamman ma na nahiyar Afurka. jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Wani abin lura a game da rubibin da ake yi na gabatar da taimako ga kasashen da bala’in ambaliyar tsunami ya rutsa da su shi ne yadda ake fatali da makomar nahiyar Afurka. misali kasar Somaliya, wacce dake daya daga cikin kasashen da bala’in ya rutsa dasu,inda a halin yanzu haka akwai mutane kimanin dubu 54 dake bukatar taimako na gaggawa a yankin Puntland, amma an yi ko oho da ita. MDD ta ce duka-duka taimakon da Somaliya ke bukata bai zarce na dala miliyan 13 ba. A can Darfur ma, ainifin abin dake hana ruwa gudu wajen cimma sulhu shi ne yadda kafofin yada labarai suka mayar da hankalinsu kacokam ga yankin Asiya."

A rikicin kasar Sudan, ko da yake an samu ci gaba wajen kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen kudancin kasar, amma har yau ana fama da fada a yammacinta. A cikin sharhin da ta rubuta jaridar Südditsche Zeitung cewa tayi:

"Makomar zaman lafiyar Sudan ta danganta ne da yadda al’amura zasu kaya a yammacinta. To sai dai kuma a halin da ake ciki yanzu babu wata alamar dake nuna cimma zaman lafiyar yankin nan ba da dadewa ba. Dukkan gwamnati da kungiyoyin ‘yan tawaye guda biyu dake fafatawa da juna ba su da iko akan dakarunsu. A yayinda Larabawan Janjaweed, mai samun goyan baya daga fadar mulki ta Khartoum, ke ci gaba da kashe-kashe na gilla da fashi da makami da kuma fyade, su ma ‘yan tawayen Darfur sun fara rikidewa domin zama ‘yan fashi da wawason ganima, inda ba ma kawai kan farar hula suke kai farmaki ba, kazalika su kan yi kwanton bauna akan manyan motocin dake dauke da kayan taimako domin kwatar ganima. A takaice kasar ta Sudan ta fara rikidewa domin daukar wani fasali irin shigen na kasar Kongo, wacce take ci gaba da fama da rarrabuwa a gabacinta, inda dakarun sa kai ke cin karensu babu babbaka. A wannan kasar babu daya daga sassan da ba sa ga maciji da juna dake da sha’awar ganin zaben da aka shirya gudanarwa a cikin watan yuni mai zuwa ya tabbata, saboda fargabar asarar kuri’a."

Ita ma kasar Uganda ta sake shiga hali na kaka-nika-yi dangane da yakin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin dakarun sojan gwamnati da na ‘yan tawayen LRA, bayan da yunkurin sulhu da aka yi a tsakanin sassan biyu ya ci tura. Jaridar Die Tageszeitung ta yi sharhi tana mai cewar:

"A daidai jajibirin shiga sabuwar shekara ta 2005 ne taron sulhu ya tarwatse tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye. Alkaluma na MDD sun ce kimanin mutane miliyan daya da dubu dari uku da talatin da hudu aka fatattaka daga yankunansu na asali a baya ga wasu miliyan biyu da dubu dari takwas da hamsin da suka dogara kacokam akan taimakon abinci daga ketare a arewacin Uganda. To sai dai kuma ko da yake yarjejeniyar tsagaita wuta ta daina aiki, amma ba a fid da kauna game da sake komawa zauren shawarwarin sulhu ba.