1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin Hajjin bana na gudana cikin nasara

October 9, 2013

Alhazzan bana na tururuwar zuwa Makka bayan kammala ziyara a Madina, domin ci gaba da sauke faralin aikin Hajji.

https://p.dw.com/p/19x5V
Thousands of Moslems attend the Friday prayer at the Great Mosque of the Haram Sharif in Mecca, Saudi Arabia, on 12 November 2010 as hundreds of thousands of pilgrims pack the area to take part in the annual Hajj (pilgrimage to Mecca). Reports state that around three million Moslem pilgrims are expected to attend this year. EPA/YAHYA ARHAB +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Maniyatan Aikin hajjin wannan shekarar ta 2013 daga sassa daban daban na duniya na kammala zamansu na ziyara a birnin Madina, inda suke daukar harama zuwa garin Makka don gudanar da Umrah da kuma Hajji nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Ana dai kyautata tsammanin maniyyata sama da miliyan biyu ne daga kassahen duniya za su gudanar da aiki Hajji na wannan shekara.

Duk da yake hukumomin kasar Saudiya sun rage yawan maniyyatan aikim Hajjin wannan shekara da kashi 20 a cikin 100, yanzu haka garin Madina sai tsiyayawa yake saboda ya zuwa yanzu kusan duk alhazzan duniya sun kammala ziyarce ziyarce a birnin Madina kuma sun isa birnin Makka ko kuma suna bisa hanya.

Na samu jin ta bakin wasu maniyyata daga Najeriya akan zamansu na Madina da kuma shirin da suke dashi na wucewa birnin makka

Su ma maniyyata mata ba a barsu a baya ba zuwa wajen Ibada, kuma sun bayyana gamsuwa da zamansu na garin Madina.

Saudi security officials wearing protective masks keep an eye on Muslim pilgrims who circle the Kaaba inside the Grand mosque in Mecca, Saudi Arabia, Tuesday, Nov. 24, 2009. An estimated 2.5 million Muslims have converged on Mecca to attend the annual hajj pilgrimage. (AP Photo/Hassan Ammar)
Hoto: AP

Riga kafin kamuwa da mura mai tsanani

Wani abu da hukumomin Saudiya suka karfafa wa maniyyata yin kaffa kaffa dashi kuwa shi ne akan bullar wata cutar mura mai tsanani da ke iya yaduwa ga alhazzai wanda ya zuwa yanzu shekara daya da bullowarta ta kama mutane fiye da 130 a cikin kasashen larabawa 8.

To ko wane tanadi ne hukumomin lafiya na Najeriya suka yi don kaucewa maniyyatansu kamuwa da irin wadannan cututtuka? Dakta Bello Abubakar wani likitan alhazzai ne a Najeriya, kuma ya ce sun dauki dukkan matakan da suka wajaba.

Su kuma jami'ai na hukumomin alhazzai na jihohi sun bayyana irin kokarin da suka yi na ganin an samu nasarar aikin wannnan shekerar.

Hukumomin Saudiya dai sun bayyana ranar Litinin mai zuwa 14 ga watan Oktoba ta kasance ranar Arafat wanda take ita ce kololuwar kammala aikin Hajji, bayan soma aikin Hajji a ranar 13 ga watannan, domin tashi zuwa gari Mina.

Mawallafi : Aminu Abdullahi Abubakar

Edita : Saleh Umar Saleh