1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai yiwuwar ganawa tsakanin Obama da Rowhani

September 23, 2013

Gwamnatin Amirka a birnin Washington ta ce ba ta fid da tsammanin shirya wata saduwa tsakanin shugaba Obama da takwaransa na Iran Hassan Rowhani ba.

https://p.dw.com/p/19mjV
Iranian President Hassan Rowhani speaks during a parliament session to elect the cabinet members on August 15, 2013 in Tehran. Iran MPs approve 15 of Rowhani's 18 cabinet picks. AFP PHOTO/BEHROUZ MEHRI (Photo credit should read BEHROUZ MEHRI/AFP/Getty Images)
Hoto: Behrouz Mehri/AFP/Getty Images

Fadar White House ta gwamnatin Amirka ta ce ba ta fid da ran yiwuwar gudanar da wani taro tsakanin shugaban Amirka Barack Obama da sabon shugaban Iran Hassana Rowhani a gefen babban taron mashawartar Majalisa Dinkin Duniya a wannan makon ba. Sai dai sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry zai halarci wani taro da wakilan manyan daulolin duniya za su yi da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif a wannan mako a kan shirin nukiliyar kasar ta Iran da ake takaddama kai. A wani labarin kuma sabuwar gwamnatin Iran ta sako firsinoni 80 wadanda aka tsare lokacin murkushe masu adawa. Wannan dai wani mataki ne na karfafa yarda ga sabon shugaban kasar Hassan Rowhnai daga kasashen yamma. Sanarwar sakin firsinonin ta zo ne sa'o'i kalilan bayan da shugaba Rowhani ya tashi zuwa birnin New York inda zai halarci taron shekara shekara na babbar mashawartar Majalisar Dinkin Duniya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh