1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alƙalai za su sa ido a ƙuri'ar raba gardama a Masar

December 3, 2012

Babbar majalisar ƙoli ta masu shari'a a Masar ta nuna aniyar sanya ido a zaɓen raba gardama kan daftarin kundin tsarin mulkin ƙasar.

https://p.dw.com/p/16v80
Hoto: dapd

Kafofin yaɗa labaru a Masar sun ce babbar majalisar shari'ar ƙasar za ta sanya ido a kan ƙuri'ar raba gardama game da daftarin kundin tsarin mulkin ƙasar da ake taƙaddama kansa, duk da ƙaurace wa zaɓen da ƙungiyar alƙalan ƙasar za ta yi. Kamar yadda tashar telebijin ƙasar ta labarto, alƙalan za su sa ido a kan zaɓen raba gardamar a ranar 15 ga watannan na Disamba. Ana dai buƙatar alƙalai da yawansu ya kai dubu 10 don gudanar da wannan aiki. Ƙuri'ar dai ba za ta zama halastacciya ba matuƙar alƙalan ba su sa ido ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar. Mohammed Gadallah, mai ba wa shugaba Mohammed Morsi shawara a kan batutuwan shari'a ya ce babbar majalisar alƙalan ta amince cewa alƙalan ke da hurumin sauke wannan nauyi da ƙasa ta ɗora musu. A ranar Lahadi ƙungiyar alƙalan ta yi kira da ƙaurace wa kuri'ar raba gardamar a kan daftarin kundin tsarin mulkin wanda a ranar Juma'a majalisar dokoki mai rinjayen wakilan 'yan'uwa Musulmi ta amince da shi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar