1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Assad zai mika makamai bisa sharadi

September 12, 2013

Shugaban Siriya ya yi alkawarin mika kai domin bori ya hau ta hanyar mika makamai masu guba da gwamnatinsa ta mallaka idan shugaban Amirka ya mayar da bakarsa ta yaki.

https://p.dw.com/p/19gmN
Hoto: Reuters

Shugaba Bashar al-Assad na Siriya ya ce kasarsa a shirye take ta mika makamai masu guba da ta mallaka karkashin kulawar kasa da kasa, da zarar Amirka ta daina barazanar afka mata da yaki da kuma taimaka wa 'yan tawaye. Cikin wata hira da ya yi da tashar telebijin ta Rasha, al-Assad ya ce ya dauki matakin ne sakamakon shawarar da Rasha ta bayar, wacce kuma ke samun goyon bayan kasashe da dama na duniya.

Da ma dai a nasa bangaren shugaban na Rasha Vladimir Putin ya gargadi takwaran aikinsa na Amirka Barack Obama game da barazanar da kai harin ke da shi ga zaman lafiya a duniya. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ke wata tattaunawa a Geneva na kasar Switzerland ko kuma Suisse kan rikicin na Siriya. Amirka na zargin gwamnatin Siriya da kashe mutane da daman gaske da makami mai guba a wani hari da ta kai a kusa da birnin Damascus a ranar 21 ga watan Agusta. Sai dai fadar mulki ta Damascus ta karyata wannan zargin, inda ta ce 'yan tawaye ne suka kai harin.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal