1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a ofishin mujalla a Faransa

Usman Shehu UsmanJanuary 8, 2015

Duniya ta yi Allah wadai da harin da ya hallaka mutane, kana ya jikkata wasu sakamakon harin da aka kai a ofishin mujallar Charlie Hebdo da ke zanen hotunan barkwanci.

https://p.dw.com/p/1EGOG
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/T. Camus

Kasar Faransa na yin zaman makoki, don girmama mutanen da suka mutu a harin da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo a Paris jiya laraba. A jawabin da ya yiwa 'yan kasar a daran jiya labarai, shugaban kasar Francios Hollande, ya ce hadin kai shi ne babban matanin da 'yan kasar za su mayar wa maharan.

Dubban 'yan kasar ne suka hallara a tsakiyar birnin Paris don nuna jimaminsu kan harin. Harin dai ya hallaka 'yan jarida goma da yan sanda biyu. Wakilin DW a Paris Georg Matthes cewa ya yi, kawo yanzu an bayyana mutanen biyu da ake kyautata zaton su ne suka kai harin a matsayin Said dan shekaru 32 a duniya da Sharif K dan 34, wadanda duk 'yan uwa ne da kuma suka yi wa anguwar da aka kai harin kekkewar sani. Wani matashi dan shekuru 18 da ya ji ana ambaton sunasa a harin, ya mika kansa ga 'yan sanda. Jaridar da aka kai wa harin dai, ta taba wallafa zanen batanci ga manzon Allah Annabi Muhammadu.

Martanin duniya

An yi gangami a biranen Turai da dama, domin nuna aljini kan harin na kasar Faransa. Dubban jama'a suka taru a biranen London, Berlin, Brussels tun a daren jiya, inda a yau Alhamis ake saran ganin garin masu gangamin, domin tunawa da wadanda suka mutu a harin na Charlie Hebdo.
Kazalika harin kusan shi ne a shafin farko na daukacin jaridun kasashen Turai.

Kurt Westergaard, dan kasar Denmark wanda shi ne ya yi zanen batanci wa manzo Annabi Muhammadu, wanda kuma shi ne zanen da mujallar Charlie Hebdo ta sake wallafawa a wacan lokacin, ya fadawa DW bayan harin na jiya cewa, lamarin da ya faru a Paris abun kaduwa ne, wanda masu tsattauran rayi suka yi. Kuma yana fatan kafafen yada labaran duniya, ba za su shiga dimaucewa ba sakamakon harin.

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois HollandeHoto: Reuters/Remy de la Mauviniere/Pool

Abin da ya faru a jiya

Harin dai an bayyana shi da mafi mune da aka kai a Faransa a 'yan shekarunnan, inda rahotanni ke nuni da cewa bisa dukkan alamu wadanda suka kai harin sun tsara shi domin sun kai harin ne a dai-dai lokacin da ma'aikatan ke taron da suka saba yi duk rana domin tsara irin ayyukan da za su gabatar, kamar yadda aka saba a ko wacce kafar yada labarai. Mujallar da aka kaiwa harin wanda aka sani da Charlie Hebdo ta taba yin zanen batanci ga Manzon Allah Annabi Muhammad (SAAW). Ko da yake mujallar ba wai addinin Musulunci ta ke yiwa batanci a sharhinta kadai ba, tama yi fice wajen sukar addinin Kirista da na Yahudawa Kawo yanzu babu tabbacin dalilin kai harin, amma shugaban kasar ta Faransa Francois Hollande tuni ya ziyarci wajen inda ya yi jawabi kamar haka....

Daukar tsauraran matakai

"Mun kunnan na'urorinmu da ke yin gargadi a kan al'amuran tsaro, mun kuma dau matakai bayan faruwar lamarin domin zakulo wadanda ke da alhaki. Za a farauto su duk inda suka shiga, kuma a gabatar da su gaban kotu a hukuntasu. Harin ya kada Faransa kuma ba dayan biyu wannan harin ta'addanci ne kan mujallar da aka yiwa barazana sau da dama, kuma take da matukar tsaro dai-dai misali. A dai-dai wannan lokacin dole mu hada kai kuma mu san yadda za mu mai da martanin da ya dace, wannan shi ne abunda za muyi cikin makwannin da ke tafe. Zan sake yi wa Faransa magana muna cikin wani yanayi mai wuya domin mun fuskanci hare-haren ta'addanci a watannin da suka gabata."

Koffi Amepete ma'aikaci ne a kamfanin wata jarida da ke birnin Ouagadougou na Burkina Faso, dake aiki makmancin na mujjalar ta Charlie Hebdo da aka kai wa hari a Fransa, ya ce wannan harin ya girgiza su matuka, musamman ganin harin ya faru a birnin Faris da ke cikakken tsaro.

Martani daga shugabannin kasashen duniya

Firaminstan Birtaniya David Cameron
Firaminstan Birtaniya David CameronHoto: Reuters/O. Scarff

Tuni dai shugabannin kasashen duniya suka yi Allah wadai da wannan hari, inda Firaministan Birtaniya David Cameron ya yiwa majalisar dokokin kasar jawabi bisa harin na Faransa kamar haka......

"Ku taya ni yin Allah wadai a kan harin dabbancin da aka kaiwa wata mujalla a Faris. Na san cewa zauren wannan majalisa da ma kasarmu baki daya, muna tare da Faransawa wajen adawa da duk nau'in ta'addanci. Kuma muna goyon bayan 'yancin fadar albarkacin baki, wadannan mutanen basu isa su hana mu wannan ba."

Ita madai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkle da shugaban kasar Amirka Barak Obama, harda sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon duk sun yi Allah wadai da wannan harin ta'addancin da aka kai a kasar Faransa. Mujjalar dai a shekara ta 2011 an taba kai mata harin bom inda aka tarwatsa ofishinta kafin daga bisani ta farfado, daga cikin wadanda suka mutu a harin na yau dai harda jami'an 'yan sanda biyu da kuma babban Editan mujallar.