1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Jamus: Shakku kan rigakafin corona

December 28, 2020

Al'umma a Jamus na tururuwa zuwa cibiyoyin da aka kebe domin karbar alurar rigakafin coronavirus da suka dade suna jira, sai dai wasu na da shakku kan yin rigakafin.

https://p.dw.com/p/3nHi8
Impfstart Deutschland Großräschen Ruth Heise
Tsohuwar da aka fara yiwa allurar rigakafin coronavirus a JamusHoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Wannan dai shi ne tsarin rigakafi mafi girma da Jamus za ta gudanar. Jami'an tsaro da na kiwon lafiya na ci gaba da aiki tukuru wajen tabbatar da an gudanar da shi lafiya. Daga jerin wadanda za a fara yi wa alurar rigakafin, su ne mutanen da ake tunanin suna kan gaba na hadarin kamuwa da cutar wadanda suka hadar da tsofaffi da kuma ma'aikatan kiwon lafiya da ke kan gaba wajen yaki da cutar.

Impfstart in Europa - Grossräschen Altersheim
Tsofaffi da ma'aikatan lafiya, cikin wadanda za a fara yi wa rigakafin COVID-19 a JamusHoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Daga ranar Lahadin da ta gabata aka fara alurar rigakafin, wacce kamfanin hada magunguna na BioNTech na Jamus da hadin guiwar kamfanin Pfizer na Amirka suka samara, bayan wasu sun an yi musu rigakafin domin kashin kansu a ranar Asabar. Daga bisani an rarraba alluran rigakafin zuwa cibiyoyin da aka tanada a kowane yanki, domin ci gaba da bayar da alluran rigakafin annobar ta coronavirus ga wadanda ke da bukata.

Karin Bayani: Merkel na fuskantar gagarumin kalubale

Ministan lafiya na kasar jamus Jens Spahn ya ce ana sa ran samun nasara babba yayin gudanar da wannan rigakafin: "Cibiyoyin bayar da rigakafin a shirye suke su fara aiki, kowa na son ganin an sami nasara a wannan tsarin rigakafin da ke zama irinsa na farko, tun bayan hadewar kasar a matsayin Tarayyar Jamus. Da yawan mutane sun kosa a fara, wannan rana ta kasance mai matukar muhimmanci ga wannan kasa ta mu."

A wani bincike da aka gudanar a kan yawan al'umma a Jamus, ya nuna cewar kaso 32 cikin 100 sun shirya yin wannan rigakafin cikin hanzari, kaso 33 cikin 100 na son su jinkirta har sai sun ga yadda kason farko suka wanye. Haka zalika binciken ya ci gaba da nuna yadda wasu kaso 19 ba su da muradin yin rigakafin kwata-kwata, yayin da kaso 16 sun kasa yanke shawara. 

Karin Bayani: Merkel ta ce a yi taka tsan-tsan

Yanzu haka dai ministan lafiyar ya yi alkawarin a cikin 'yan kwanakin da ya rage a wannan shekarar, za a samar da sama da miliyan guda na allurar. Al'umma da dama na fatan samun kariya, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun yawaitar masu dauke da cutar. Jamus na samun kusan mutane 1000 a kullum da ke mutuwa, lamarin da ya sa mutane fargabar shagulgulan Kirsimeti da na sabuwar shekaraka iya dawo da cutar a karo na uku.