1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben 'yan majalisar a Birtaniya

Sani DaudaMay 6, 2015

Cece ku ce kan batun baki da za a bari su shiga kasar ta Birtaniya na zama kan gaba wajen yakin neman zaben 'yan majalisar dokokin kasar .

https://p.dw.com/p/1FKzj
Großbritannien David Cameron Wahlkampf 2015
Firaminista David CameronHoto: Reuters/T. Melville

A kasar Britaniya, a ranar Alhamis ce al'ummar kasar za su kada kuri'ar sabuwar gwamnatin da za ta ja ragamar mulkin kasar har tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Bisa al'ada dai a Britaniya zaben gwamnatin da za ta yi mulki mafi yawa yakan dogarane kan karfin tattalin arzikin kasa. To amma a wannan karon batun baki da ke zuwa nan Britaniya ko dai da nufin ci rani ko kuma domin zaman din-din-din, ko kuma 'yan gudun hijira, shi ne ya mamaye zaben a wannan karon. wannan kuwa ya samo asali ne bisa karin farin jinin wata karamar jam'iyyar siyasa da akafi sani da UKIP, jam'iyyar da ke neman Britaniya ta fice daga Tarayyar Turai.

Prayim Minista David Cameron, kuma shugaban Jam'iyyar da ke mulki ta Conservative, ya ce idan aka sake zabensa to kuwa zai tabbatar cewa ya sami amincewar sauran kasashen Turai domin rage yawan mutanen da zasu rika shigowa Britaniya duk shekara zuwa dubu dari kawai.

Shi kuwa shugaban babbar Jam'iyyar adawa ta Labour Party, Mr. Ed Miliband, mayar da martani ya yi kan burin UKIP na ficewa daga Tarayyar Turai:

Nicola Sturgeon Wahl als Parteivorsitzende der SNP Partei Schottland 14.11.2014
Nicola Sturgeon jagorar jam'iyyar SNPHoto: Reuters/C. McNaughton

"Ficewar Britaniya, daga tarayyar Turai abu ne da zai zama babbar Annoba ga kasarmu ".

To amma jam'iyyar da ake ganin za ta bayar da mamaki musamman a mazabun kasar Ingila ita ce Jam'iyyar da ke fatan ficewar Britaniya daga Tarayyar Turai ta UKIP. Shugaban jam'iyyar, Mista. Nigel Farage, ya danganta matsalolin rashin isassun gidaje, da rashin aikin yi da matsalar koma bayan rayuwa ga baki da ke kwararowa daga Turai da sauran kasashen Duniya:

"Ba daidai bane, a lokacin da tsoffinmu da al'ummarmu ke matse aljihunsu, baki su rika zuwa suna samun kiwon lafiya kyauta ba. inda ya kara da cewa musamman baki dauke da kwayoyin HIV da ke haddasa cutar Aids suke zuwa Britaniya a ba su magunguna masu tsada kyauta".

UK Salford Wahlen TV Debatte Kandidaten Parteien
'Yan takara a zaben BirtaniyaHoto: Ken McKay/ITV/Handout via Reuters

A ranar Alhamis ne dai za'a tantance kan irin rawar da Jam'iyyun za su taka, musamman ganin zaben jin ra'ayi na kasa na nuni da cewar babu jam'iyyar da za ta sami cikakken rinjaye, a tsakanin manyan jam'iyyu uku, Conservatives da Labour da Liberal Democrats.