1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar duniya na yin bukukuwan Kirismati

December 25, 2016

Dubban mabiya addinin Kirista sun halarci taron addu'o'i a birnin Bethleem wanda ke zama mahaifar Annabi.

https://p.dw.com/p/2UrEC
Bethlehem Weihnachten Messe
Hoto: Getty Images/H.Bader

Daga nasa bangare a hudubar da ya gabatar a daran jiya Asabar a fadarsa ta Vatican a gaban mutane dubu 10, Paparoma Francis jagoran Kiristoci mabiya darikar katholika a duniya ya yi kira ga a tausaya wa kananan yara musamman wadanda yake-yake dama talauci ya saka a cikin halin kunci inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

" Muna da babban kalubale a gabanmu na kananan yara, ka dauka tun daga wadanda aka tauye wa 'yancin zuwa duniya da wadanda ke kuka sabili da yunwa da wadanda suka rasa kayan wasa a hannunsu sai dai makamai."

Sai dai a kasashen Turai da dama ana ci gaba da gudanar da shagulgullan bikin Kiristimetin  na bana a cikin tsaurararn matakan tsaro sabili da fargabar da ake da ita ta yiwuwar fuskantar hare-haren ta'addanci kasancewa bikin ya zo ne kwanaki kalilan bayan harin da aka kai a kasuwar Kiristimatin birnin Berlin na kasar Jamus da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12.