1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Faransa na dakon sabuwar majalisar zartarwa .

August 26, 2014

Nan da sa'oi ne dai ake saran bayyanar sabuwar majalisar ministocin da shugaba Hollande na Faransa zai kafa. Wani yunkuri na farfado da martabar jamiyyar shugaban mai ra'ayin gurguzu.

https://p.dw.com/p/1D1Jp
Francois Hollande und Arnaud Montebourg
Hoto: Alain Jocard/AFP/Getty Images

Bayan rushewar da aka yi wa majalisar da ta zo ba tsammani, a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama kan tsare-tsaren tattalin arziki da su ke dada samun koma baya a wannan kasa.

Ko da yake tuni matsalar rashin aikin yi tayi katutu a zukatan al'umma, ga rashin samun tagomashi a tattalin arziki, mai yuwuwa shugaban kasa Francois Hollande ya yi amfani da wannan dama ta yin garan bawul a majalisar ko da ya sake bada karfin gwiwa kan ayyukan wannan jamiyyata tasu mai ra'ayin gurguzu.

Wannan yunkuri dai na shugaba Hollande na iya zama dama ta karshe a gareshi wajen bada kariya ga mulkinsa na tsawon shekaru biyar a Faransa.

Wasu majiyoyin na fadar Elysee ta shugaba Hollande kuwa sun fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa shugaban ya dauki wannan mataki ne dan ganin ya kafa wa kasar alkibla mai kyau.

Nan da sa'oi ne dai ake saran bayyanar sabuwar majalisar ministocin da shugaba Hollande zai kafa a wannan kasa.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita :Umaru Aliyu