1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Kenya na jiran sakamakon babban zaben

August 8, 2017

A wannan Talatar ce al'ummar kasar Kenya suka yi dafifi a rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa don zaben wanda zai jagoranci kasar bayan cikar wannan wa'adi.

https://p.dw.com/p/2htoy
Kenia Wahlen in Nairobi
Hoto: Reuters/T. Mukoya

A zaben dai ana karawa ne tsakanin mayan 'yan takara kuma masu adawa da juna wato shugaba mai ci Uhuru Kenyata da babban mai hamayya da shi Raila Odinga. Duk da cewa kasar ta Kenya ta fuskanci rikicin zabe a baya, tuni manyan 'yan takarar biyu suka bayyana cewa za su amince da sakamakon zaben, inda su kayi kira ga magoya bayansu da su guji duk wani abu da ka iya ta da hankula.

Wannan shi ne karo na biyu da 'yan takarar ke fafatawa da juna, kuma kuri'ar jin ra'ayi ta nuna cewa ana iya yin kan-kan-kan da juna. Tun cikin daren da ya gabata ne alummar kasar suka fara shiga dogayen layuka duk da irin sanyi mai tsanani da ma ruwan sama da aka samu a wasu yankunan kasar.  Alamu kuma na nunin cewa kabilanci na taka rawa a zaben, inda galibin 'yan kabilar kikuyi ke kada kuri'unsu ga shugaba Kenyatta, inda a gefe guda 'yan kabilar Lou ke zaben madugun adawa Raila Odinga.

Kenia Kisumu Proteste
Hoto: DW/J. Marwa

Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa an samu matsalar tsaro a wasu mazabu uku da ke yankin Laikipia, sai dai ta ce tuni jami'an tsaro suka shawo kan lamarin inda a ka ci gaba da kada kuri'a. A cewar hukumar zaben duk da cewa za a rufe runfunan zaben da zarar lokaci ya yi, za a bar wadanda ke jira akan layi su kada kuri'unsu.

Sai dai wasu rahotannin na cewa a yankunan Baringo da Turkana da kuma yankin arewacin kasar ruwan sama ya kawo tsaiko wajen raba kayan zaben, amma hukumar zaben ta ce za a kara lokutan rufe runfunan zaben a wuraren da aka samu matsalar fara zaben a kan lokaci. Ana ma nazarin yiwuwar kai zaben zuwa ranar Laraba. A dai dai wannan lokacin dai an soma samun wasu runfunan zaben da suka rufe tun karfe biyar agogon kasar ta kenya.

Tsohon shugaban kasar Ghana kuma shugaban tawagar sa ido na kungiyar kasashe renon Ingila, John Mahama, ya nuna gamsuwa da yadda masu zabe suka fito don kada kuri'ar a wannan rana mai muhimmanci ga kasar ta Kenya. Fatan 'yan kasar dai shi ne a kare zaben cikin lumana.