1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Sudan sun fara jefa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasa.

April 11, 2010

Jama'ar Sudan sun fara jefa ƙuri'unsu a zaɓukan farko daya ƙunshi jam'iyyu da dama cikin shekaru 24

https://p.dw.com/p/Msz6
Wani ɗan Sudan na jefa ƙuri'ar sa

Yau - lahadi ne al'ummar ƙasar Sudan ke zuwa runfunan zaɓe domin ka'ɗa ƙuri'un su, a zaɓukan da ƙasar zata kwashe tsawon kwanaki ukku tana yi, wanda kuma ya ƙunshi jam'yyun siyasa da dama. Wannan dai, shi ne zaɓe na farkon da Sudan ke gudanar wa tun cikin kimanin shekaru 25 a ƙasar data daɗe tana fama da yaƙin ba'sa'sa. Hukumomin ƙasar dai, sun tsaurara matakan tsaro, sai dai kuma tuni zaɓukan dake zama abin tahiri a ƙasar, kasancewar ya ƙunshi jam'iyyu da dama ya sami koma baya saboda zarge - zargen yunƙurin tafka magaɗin da wasu jam'iyyu da kuma 'yan takara suka yi, lamarin da ya sa wasunsu janyewa daga takarar. Ana sa ran shugaba Umar Hassan al-Bashr dake kan mulki ne zai lashe zaɓen, domin muhimman masu ƙalubalantar sa sun janye takarar su.

Tuni dai jagorar yankin kudancin Sudan Silva Kiir ya jefa ƙuri'ar sa a kudancin birnin Juba - a dai dai lokacin da masu sanya ido na ƙasa da ƙasa ke duba yadda zaɓukan, wanda ya haɗar dana majalisar dokoki da kuma na ƙananan hukumomi ke gudana.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh