Amílcar Cabral da yunkurin neman 'yanci

A fafutukarsa ta kishin kasa, Amílcar Cabral ya jagoranci Gini Bissau da Cape Verde wajen samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, amma an hallaka shi kafin hakarsa ta cimma ruwa.

Rayuwarsa:

An haife shi a shekarar 1924 a Bafata da ke Gini Bissau. Mahaifansa 'yan asalin kasar Cape Verde ne kuma ya girma a Sao Vicente da ke kasar ta Cape Verde. Ya karanci ilimin tsirrai a birnin Lisbon na kasar Portugal kafin daga bisani ya koma Gini Bissau. An hallaka Cabral ne a ranar 20 ga watan Janairu na shekarar 1973 a birnin Conakry na kasar Gini.


Shaharar da ya yi: 

Yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar nan ta PAIGC a shekarar 1956. Jam'iyyar ta yi fafutuka ne wajen ganin kasashen Gini Bissau da Cape Verde sun samu 'yancin kai kuma Cabral din ne magatakardar jam'iyyar. A lokacin da yake rike da wannan mukamin ya yi fafutuka wajen hada kan kasashen biyu a yakin da ake yi da Turawan mulkin mallaka. Jam'iyyar ta PAIGC ta taimaka an samu mulkin kai a Gini Bissau a shekara ta 1973. Cabral dan kishin kasa ne kana masanin harkar gona sannan marubucin waka ne a zamaninsa.

Sukar da aka rika yi masa: 

Kin amincewa da shigar da wasu dabaru daga waje don yin amfani da su wajen fafutukar samun 'yancin kai a Gini Bissau.


Abin koyi: 

Amílcar Cabral ya kasance mutum abin koyi a lokacin da ake fafutukar neman mulkin kai ba wai a kasashen da ke magana da harshen Portuguese a Afirka ba, har ma da sauran sassan duniya. A Lisbon, Cabral ya taimaka wajen kafa kungiyar nan ta Centro de Estudos Africanos, wadda mambobinta dalibai ne da suka fito daga kasashen Afirka da ke magana da harshen Portuguese a Afirka, sannan ya yi ta hulda da jiga-jigai a irin wadannan kasashe da ke fafutuka ta neman mulkin kai. Irin wadannan mutane sun hada da Agostinho Neto da Mário Pinto de Andrade da kuma Marcelino dos Santos.

Now live
mintuna 01:28
Tushen Afirka | 16.08.2018

Amilcar Cabral-jagoran samun 'yancin kai na kasashen Gini ...

Kalamansa mafi shahara:

"'Yan Afirka sun san cewar maciji zai iya sauya fatarsa amma kuma hakan ba zai sa ya tashi daga matsayinsa na maciji ba."

"Ba mu taba sanya al'ummar Portugal da Turawan mulkin mallakar Portugal kan mizani guda ba. Fafutukar da muka yi da 'yan mulkin mallaka ne ba al'ummar Portugal ba."

"In har wani zai min illa to wanda zai yi din zai kasance ne a cikinmu. Ba wanda zai iya illata PAIGC in ba mu ba."


Tababa:

An hallaka Amílcar Cabral a Conakry kuma ana zargin wani mamba ne na jam'iyyarsu ya yi haka bisa umarnin Turawan mulkin mallaka na Portugal. Wannan batu ya jawo tababa game da wanda ke da hannu kan kisan Cabral. An ce an san wanda ya hallaka shi amma kuma ba tabbaci game da wanda ya ba da umarnin kisan.


Wannan bangare ne na shiri na musamman Tushen Afirka "African Roots", shirin hadin gwiwa tsakanin tashar DW da Gidauniyar Gerda Henkel.