1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya na ci gaba da barna a Najeriya

August 31, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce kimanin 'yan kasar mutum dubu 500 ne ambaliyar ruwa ta shafa tun shigowar daminar bana zuwa halin da ake ciki.

https://p.dw.com/p/4GFj4
Nigeria Kebbi | Überschwemmung zerstört Ernte
Hoto: DW

Ofishin Shugaba Buharin ya ce gwamnati na sama wa wadanda ambaliyar ta shafa tallafi na gaggawa, kamar yadda yake ci gaba da karbar bayanai a kai a kai dangane da ta'adin da ake samu.

Jihohi 23 cikin 36 na ne dai ambaliyar ta shafa a Najeriyar, inda lamarin ya fi muni a jihohin Arewa maso Gabashin kasar.

Sama da mutum 100 ne dai suka mutu wasu 270 suka jikkata yayin da mutum dubu 73 su ne ambaliyar ta raba da gidaje, sannan a gefe guda akwai gonaki a cewar Shugaba Buhari cikin wata sanarwa.

Galibi dai mutane kan fama da matsalar ta ambaliya a Najeriya a lokutan damina, kama daga watan Mayu zuwa Satumba.