1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ruwan saman a ƙasar Chaina

June 17, 2010

Mutane 46 suka rasa rayukansu yayin da wasu guɗa 50 suka ɓata a kudancin ƙasar Chaina

https://p.dw.com/p/Ntgy
Hoto: dpa - Report

A ƙalla mutane 46 suka mutu yayi da wasu guda 50 suka ɓata a sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ake sheƙawa a kudancin ƙasar Chaina waɗanda suka hadassa ambaliya.

Offishin ministan harakokin waje na ƙasar da ya baiyyana adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su, ya shedda cewa tun a ranar lahadi an ƙwashe sama da mutane  dubu 240 a cikin wasu garuruwa shidda na yankin kudancin na kasar yayin da gidaje kamar dubu 33 suka ruguje.

Ruwan saman dai da ake sheƙawa a kasar ba dare ba rana a 'yan kwanakin nan   sun tilassawa hukumomin kula da al' amuran sufiri na kasar soke tashin jiragen sama 314 yayin da wasu tashin 489 aka ɗakasu haryazuwa wani lokaci.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane.

Mawallafi : Abdullahi  Tanko  Bala.