1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa : Ana buƙatar dala miliyan 38 don bada tallafi a Najeriya

November 9, 2012

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana bukatar dalar Amurka miliyan talatin da takwas domin bada agaji ga mutane miliyan biyu da dubu dari wanda ambaliyar ruwa ta shafa a Najeriya.

https://p.dw.com/p/16g7r
Hoto: picture-alliance/dpa

Mai magana da yawun babban jami'in hukumar kula bada agaji ta Majalisar ta Ɗinkin Duniya Jens Laerke ya ce bayan ga batun neman muhalli ga wadanda amabaliyar ruwan ta raba da matsugunansu, a cikin tsarin da aka yi akwai batun samar da abinci da tsabtataccen ruwan sha da gyara makarantu a yankunan da ake da yawaitar gonaki da kuma wuraren da masunta su ka fi yawa musamman ma dai ƙauyukan da ke daura da kogin Naija.

Ambaliyar ruwan da aka yi dai a tarayyar ta Najeriya kamar yadda alkaluman hukumar bada agajin gaggawar ƙasar ta NEMA su ka nuna, kimanin mutane ɗari uku da sittin da uku ne su ka rigamu gidan gaskiya yayin da mutane dubu sha takwas su ka jikkata baya ga asara ta amfanin gona da aka yi ta ɗumbin miliyoyoyin Naira.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammed Awal Balarabe