1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'adin ruwa a kudancin Afirka

Ahmed Salisu
March 22, 2019

Iska mai karfi hade da ambaliyar ruwan sun yi sanadin rasuwar mutane da dama a yankin kudancin Afirka musamman akasashen Muzambik da da Zimbabuwe da kuma Malawi.

https://p.dw.com/p/3FVXn
Mosambik Buzi Nach Zyklon IDAI
Hoto: Getty Images/AFP/A. Barbier

Karon farko kenan da kasashen na Kudancin Afirka suka gamu da matsala irin wannan wadda ta girgiza su. Jami'an Majalisar Dinki Duniya musamman wadanda ke aiki da hukumar abinci ta Majalisar sun ce mutane kimanin miliyan guda da rabi ne ke cikin hali na tsaka mai wuya a kasashen sai dai kasar Mozambik na kan gaba wajen yawan wadanda wannan Iftila'i ya fi shafa.

Ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ta tabbbatar da rasuwar mutane 84 a hukumance amma kuma shugaban kasar Filipe Nyusi ya ce bisa ga abinda idonsa ya gane masa akwai yiwuwar yawan wadanda suka rasu din ya karu sannan jama'a da dama a halin yanzu na cikin mawuyacin hali.

Mosambik Wirbelsturm «Idai»
Hoto: Reuters/IFRC/RED CROSS CLIMATE CENTRE

Galibin wadanda lamarin ya shafa dai suka ce cikin dare ne suka ankara bayan da ruwa ya fara cika gidajensu kafin kuma daga bisani iska mai karfin gaske ta fara yaye rufin matsugunansu. Wata budurwa 'yar shekaru 14 da abin ya shafa ta ce abincinsu da kayan karatunta duk sun salwanta sakamakon wannan matsala da kasar tasu ta Mozambik ta fuskanta.

Yanzu haka dai kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa na cigaba da kokari wajen ganin sun bada tallafi ga yankin da lamarin ya shafa musamman ma dai birnin Beira inda kashi 90 cikin 100 na gidaje suka rushe yayin da saura suka cika makil da ruwa.

Masana hasashen yanayi na cewar akwai yiwuwar sake fuskantar ambaliyar ruwa, lamarin da ya sanya ake kiraye-kiraye ga sauran kasashe da su tashi haikan wajen ganin an tallafa wa Mozambik da sauran kasashen da abin ya shafa.