1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Sudan: Asarar rayuka a ambaliyar ruwa

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 31, 2022

Mahukuntan Sudan sun sanar da cewa mummunar ambaliyar ruwa da ta afku sakamakon mamakon ruwan sama a kasar, ta halaka mutane kimanin 100 tun bayan faduwar damuna a watan Mayu.

https://p.dw.com/p/4GGuS
Ambaliyar Ruwa | Sudan
Ambaliyar ruwa na ci gaba da yin barna a SudanHoto: Sami Alopap/AA/picture alliance

Mai magana da yawun rundunar tsaron farar hula ta kasar Janar Abdul-Jalil Abdul-Rahim ya bayyana cewa ambaliyar ruwan, ta kuma raunata kimanin mutane 96 kana gidaje dubu 27 da 600 sun rushe yayin da wasu dubu 42 suka lalace. Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane dubu 258 ambaliyar ta shafa a gundumomi 15 na kasar ta Sudan, tare da shafe kauyuka da dama da kuma dubban gonaki. Tuni dai Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasar, ta kai dauki a gundumomi shida da iftila'in ambaliyar ya fi shafa. Acewar Ofishin Kula da Bayar da Agaji na Majalisar Dinkin Duniya, yankunan sun hadar da yammacin yankin Darfur da yankin Kogin Nilu da yammaci da kuma kudancin Kordofan. A bisa al'ada dai damuna na sauka a Sudan ne cikin watan Yuni har zuwa karshen watan Satumba, sai dai a bana ta sauka tun a watan Mayu.