1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta kashe sama da mutum 20 a Iran

July 23, 2022

Kasar Iran na cikin kasashen da ke fuskantar karancin ruwan sama, lamarin da ke haifar da mummunan fari. Amma kuma lokaci zuwa lokaci, ambaliyar ruwa kan mamaye gidaje a duk lokacin da aka yi mamakon ruwan sama.

https://p.dw.com/p/4EYRJ
Iran Teheran Militärparade Präsident Ebrahim Raisi
Hoto: President Website/WANA/REUTERS

Ambaliyar ruwa ta halaka akalla mutane 21 a kudancin kasar Iran. Shugaban kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a yankin Estahbah, Hossein Darvishi, ya ce akwai karin wasu mutane da ba a ji duriyarsu ba tun bayan da ambaliyar ruwan ta afku. A yayin da suke tabbatar da faruwar ifti'alin a wannan Asabar, hukumomin yankin sun ce tsakiyar lardin  Estahbah ne ambaliyar ta fi yi wa ta'adi.

A shekara ta 2019, ambaliyar ruwa irin wannan ta yi ajalin mutum 76 a kudancin Iran sannan ta haddasa wa magidanta asarar da ta kai darajar kudi Dala miliyan 2000.