1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita ta koyar da harsunan gida

Zainab Mohammed Abubakar Tabea Goppelt
September 25, 2018

Da yawa daga cikin yaran Afirka ba sa fahintar abin da malamansu ke fadi a matakin farko na shiga makaranta. Harsunan Turai kamar Turanci da Faransanci ko Potugis ake musu darasi. Kasashe da dama na neman mafita.

https://p.dw.com/p/35SYk
Entwicklungshilfe Afrika
Hoto: picture-alliance/ZB

A kasashen Afirka da ke yankin kudu da Sahara, akwai harsuna daban-daban da yawansu ya kai 2,000. Ana magana da su a gidaje, kan tituna da ma gidajen rediyo da Talabijin, amma kalilan ne suka samu shiga cikin ajujuwa a makarantu.

Harsunan da ake amfani da su a makarantu dai, sun kasance na kasashen da suka yi mulkin mallaka a Afirka, kuma akasarin yaran da ke zuwa makaranta ba su da masaniya dangane da harsunan, kafin su shiga makaranta.

Kwararru a fannin ilimi dai sun nunar da cewar wannan hanyar koyarwar ba ta dace ba. Kwararriya kan ilimi a Norway Birgit Brock-Utne ta yi tsokaci..

"Idan kana neman hanyar hana yara koyon karatu, ka riga ka samu, idan kana yi musu darasi cikin harsunan da ba kasafai suke jinsu a kewayensu ba. Kuma a yawancin lokuta, su ma malaman ba su iya harshen sosai ba. Akwai kura-kurai masu yawa, kuma idan suka zo rubutu ma akwai kura-kurai kamar yadda muke yawaita gani".

Sprache der Zukunft: afrikanische Schulklasse mit Galeriebild Flagge Kamerun

To sai dai a wasu kasashen Afirka an fara samun sauyi a ajujuwa. A matakan firamare ana sanya harsunan gida cikin jadawalin karatu, a yayin da wasu lokutan ana koyar da darussa kacokan cikin harsunan uwa.

Rahoton shekara ta 2016 na Asusun kula da ilimin yara na MDD watau UNICEF, ya jaddada muhimmancin koyar da darussa cikin harshen uwa, musamman a matakin firamare. A cewar UNICEF wajibi ne yara su koyi karatu cikin harshen uwa na tsawon shekaru shida, domin hakan ne zai taimaka dorasu kan turbar fahintar abin da ake koya musu.

Wata matsala ita ce, zabar harshen uwa a kasashen da ke da harsuna da yawa, alal misali Najeriya, inda ake da su sama da 500, kuma ake amfani da Turancin Ingilishi a matsayin harshen koyarwa a makarantu. A yanzu haka an kaddamar da wani gagarumin shiri na koyar da manyan harsunan kasar guda uku cikin jadawalin makarantun firamare, watau Hausa da Igbo da Yarabanci.

BdT Scrabble WM in Afrika Frankreich verliert in französischer Sprache
Hoto: AP

Yawancin yara na tasowa ne a yankunan da ake da harsuna masu yawa, don haka ya zamanto wajibi malamai su kasance masu la'akari da hakan, Rose Marie Beck, farfesa ce a sashin nazarin Afirka a jami'ar Leipzig da ke Jamus:

"Zai fi dacewa a yaran su koyi karatu a harshunan da suka sani. Amma ayar tambayar anan ita ce, wane harshe ke nan."

A Senegal da Faransanshi ake koyarwa a makaranta, kasar da al'ummarta kashi daya daga cikin uku ne kadai ke magana da Faransanci sosai. Yanzu haka an kaddamar da shirin bayar da darasi cikin Faransanci da a kalla wani harshe daya na kasar. Haka zalika kasar Mozambik na shirin kaddamar da harsunan kasar 23 cikin jadawalin karatu.

Sai dai wannan mataki na bukatar kudade masu dumbin yawa. Duk da cewar akwai kungiyoyin kasa da kasa kamar su  La Francophonie da USAID na Amirka da ke gudanar da shirye-shirye na tallafawa ilimi da horas da malamai, da sauran tafiya a kokarin sanya harsunan gida cikin jadawalin karatu a kasashen Afirka.