1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da kimiya wajen bunkasa Afirka

Wanjiru/A: Brigitte Osterath/Yusuf IbrahimMarch 16, 2016

Inganta fannin kimiya da fasaha na nahiyar Afirka domin samar da ci-gaba mai dorewa.

https://p.dw.com/p/1IDxH
USA Patrick Awuah vom Ashesi University College
Hoto: DW/B. Osterath

A kwanakin baya ne masana kimiya a fadin duniya suka gudanarda wani taro a birnin Washington DC da ke kasar Amurka domin tattaunawa game da bincikensu, babban kudirin da aka tattauna shi ne yanda za a inganta fannin kimiya da fasaha a kasashen nahiyar Afirka.

Shi dai wananan taro nada nufin bada kwarin gwiwa ga nahiyar Afirca ta yadda zasu fadada bincike game da fannin kimiya da fasaha domin magance wasu matsaloli da ka iya tasowa nihiyar kuma hakan ka iya taimakawa ta kasance ajin farko wajen gudanar da bincike.

Patrick Awuah na daya daga cikin mahalarta taron kuma dan Afirika ne ya sha alwashin ganin ya cimma burinsa na kawo canji a Afirka a fannin kimiya da fasaha, yana mai cewa:

"Na taso a Ghana na kuma yi karatu a wata kwaleji a Amurka, na kuma yi aiki a kamfanin manhajar microsoft, saboda haka na yanke shawarar koma gida in taimaka wajen ci-gaban nahiyata, ko dayake idan na na fara gina wata kolaji wadda za ta mayar da hankali kan ilmantar da masana kan harkokin kasuwanci, da mutane masu warware matsaloli wadanda suka damu da al'umma ina ganin ta haka za mu iya canza nahiyar"

A shakara ta 1999, Awuah ya samar da wata jami´a mai suna Ashesi, da koleji mai zaman kanta ta birnin Accra da ke kasar Ghana, ana gudanar da digiri a tsawon shekaru hudu a faononi daban-daban kamar, fannin, ilmin na'ura mai kwakwalwa wato kwamfuta, da aikin injiniya, da kuma fannin hada -hadar kasuwanci, kamar yadda Awuah ya kara bayyanawa:

"Mun yaye wadanda suke aiki a bankuna daban-daban wadanda aka tura fannin na'ura mai kwakwalwa kuma an samu ci-gaba a bankunan matuka. Mun kuma yaye wadanda ke aiki fannin gine-gine da kuma masu aiki fannin rigistar na'ura mai kwakwalwa, wanda kuma hakan ka iya kawo gagarumar gudummuwa wajen gudanar da zabukammu tsab babu matsala"

Awuah ya kara da cewa wada daliba daga cikin wadanda suka yaye sun tura a wani fannin da suka bude na koyarda yara maza da mata wadanda suka kasance marayu tana koyar da su ilmin na'ura nai kwakwalwa. Jami'ar nada rassa a kasashe irinsu, Senegal da Ghana da Kamaru da Tanzaniya da Afirka ta Kudu manufar yin haka shi ne domin habaka ilmin kimiya da fasaha a nahiyar Afirka.