1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Tallafawa marasa lafiya ta shafukan sada zumunta

February 21, 2020

Shirinmu na Lafiya Jari a wannan jikon ya mayar da hankali kan yadda matasa ke amfani da shafukan sada zumunta wajen tallafawa marasa lafiya da basu da isassun kudi na neman magani.

https://p.dw.com/p/3Y9TP
Symbolbild Twitter
Hoto: Imago/xim.gs

Matasa da dama a Najeriya kan yi amfani da shafukansu na sada zumunta don agazawa wanda ke jinya kuma basu da wadatattun kudi na sayen magani. Fauziyyah D. Sulaiman na daga cikin wanda suka yi fice a wannan harka a jihar Kano da ke arewacin kasar. Ta na da mabiya dubu 160 a shafinta na Instagram, sannan rubutunta na neman taimako ga marasa lafiya kan kai ga mutane 5000 a shafin facebook a cikin kankanin lokaci. Ta ce burinta shi ne ta yi amfani da yawan jama’anta a intanet wurin ceton rayukan jama’a. Ta yi mana bayanin yadda aikin nata ke gudana kuma za a iya saurarar cikakken shirin a nan kasa.