1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Matashiya ta rungumi sana'ar lalle

Aliyu Muhammad Waziri
November 7, 2018

Wata matashiya da ta yi karatu har ta kammala a jami'a ta rike sana'ar lalle irin na zamani a Bauchi da ke Najeriya.

https://p.dw.com/p/37pG7
Henna-Tatoos
Hoto: Imago/Danita Delimont

Wata matashiya da ta yi karatu har ta kammala a jami'a ta rike sana'ar lalle irin na zamani da ake kira Dayis wadda ta bude kamar wata masana'anta a cikin gidan su da yanzu haka ma take da wasu 'yan mata da suke koyon irin wannan sana'a.

Matashiyar mai suna Fatima Zubairu wacce aka fi sani da Mummy mai lalle ta bayyana cewa bukatar ganin ta samu abin dogaro da kanta shi ne dalilin da ya sa ta fara wannan sana'a ta lalle.

Mummy ta yi karatun ta a jami'a har ta kammala, wadda kuma mafi akasarin matasa ire-irenta wadanda sukayi karatu sun fi raja'a da jiran sai gwamnati ta ba su aikin yi wadda kuma a irin wannan lokaci yake da matukar wahalar samu.