1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano dan Kenya na ba wa IS kudade

Yusuf Bala Nayaya
September 7, 2018

Sashin baital malin Amirka ya bayyana sunan wani dan kasar Kenya cikin bakin littafi na masu daukar nauyin aiyukan 'yan ta'addar kungiyar IS a duniya.

https://p.dw.com/p/34ViV
Syrien IS Kämpfer bei Hama
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com

Sashin baitul malin na Amirka ya bayyana sunan Waleed Ahmed Zein wanda aka kama a Nairobi a watan Yuli a matsayin wanda ke tura kudade zuwa ga 'yan ikirarin Jihadin na IS.

Zein wanda karkashin dokar Amirka aka bayyana shi "da zama dan ta'adda na musamman " wanda alaka da shi ma na iya jaza wa mutum binciken kwakwaf, an zarge shi da tura kudade da suka kai Dala dubu 150, zuwa ga rassan na IS tsakanin 2017 zuwa 2018 don tallafa wa mayakan a Siriya da Iraki da Libiya da Afirka ta Tsakiya.

A cewar masu sanya idanun kan motsin masu daukar nauyin aiyukan na ta'addanci daga Turai da Gabas ta Tsakiya da Amirka da Afirka ta Gabas Zein mutum ne da ke da hadari sosai.