1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na ƙara yin matsin lamba ga Isra'ila

March 15, 2010

Amirka ta buƙaci Isra'ila ta soke shirin gina ƙarin matsugunai baki ɗayansa

https://p.dw.com/p/MSwH
Mataimakin shugaban Amirka Joe Biden da Frime Minista NatanyahuHoto: AP

Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun sanar da cewar, Amirka na yin matsin lamba ga Isra'ila data yi watsi da shirinta na gina ƙarin matsugunan yahudawa 'yan kama wuri zauna a yankin gabashin birnin Jerusalem. Hukumomin Isra'ila sun amince da shirin gina sabbin matsugunai 1,600 ne a lokacin rangadin mataimakin shugaban Amirka Joe Biden - cikin makon jiya, lamarin da a birnin Washington, ke ganin a matsayin cin fuska ne a garesu, da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiyar da suke yi a yankin, game da sake komawa kan teburin sulhu a tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa. Yau Litinin, wasu Jaridu da kuma tashoshin Rediyon Isra'ila sun sanar da cewar, Amirka na son ganin Isra'ila ta soke shirin baki ɗayansa. Falasɗinawa sunƙi amincewa da aikin gina sabbin matsugunai a yankin, domin suna son gabashin Jerusalem ya kasance hedikwatar ƙasarsu. Shi kuwa Frime Ministan Isra'ila Benjamin Natanyahu na yin adawa ne da rarraba birnin na Jerusalem kana yana son birnin ya kasance a ƙarƙashin ikon Isra'ila kaɗai.

A wani ci gaban kuma, a yau Litinin ne Kantomar kula da harkokin ƙetare a ƙungiyar tarayyar Turai, Catherin Ashton, ke fara ziyarar aiki a yankin na Gabas Ta Tsakiya, a ƙoƙarin da itama ƙungiyar ke yi na samar da zaman lafiya a yankin, da kuma tantance yadda ake tafiyar da kuɗaɗen agajin da take turawa can. 

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas