1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na buƙatar a tsagaita wuta a Siriza

Abdourahamane HassaneFebruary 11, 2016

Ministocin harkokin waje na ƙasashen da ke da hannu a yaƙin da ake yi a Siriya sun soma gudanar da wani taron na samar da hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin Siriya.

https://p.dw.com/p/1Hu7W
Münchener Sicherheitskonferenz 2015 Kerry Ankunft
John Kerry ministan harkokin wajen AmirkaHoto: Reuters/M. Dalder

Taron wanda ke gudana a birnin Munich da ke a nan kudancin Jamus ana sa ran Amirka da sauran ƙawayenta za su samu damar yin ƙarin matsin lamba ga Rasha da ta tsagaita wuta.

Tun farko gwamnatin Rasha da ke goyan bayan gwamnatin Bashar Al Assad ta yi furcin cewar a shirye take ta dakatar da bude wuta,to amma Amirka ta ce ta na buƙatar a dakatar da buɗe wutan nan take.