1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta buƙaci China ta martaba haƙƙin 'yan Tibet

September 28, 2011

Bayan da wasu limaman addinin Budha suka ƙona kansu don nuna rashin amincewa da mulkin China a Tibet , Amirka ta yi kira ga Chinan da ta martaba haƙƙin 'yan wannan yanki

https://p.dw.com/p/12ia2
Wani matashin ɗan Tibet ɗauke da tutar wannan yankiHoto: DW

Amirka ta yi kira ga kasar China da ta martaba haƙƙin al'umar yankin Tibet ta kuma biya musu buƙatunsa . Amirka ta yi wannan kiran ne bayan da wasu limaman addinin Budha biyu suka ƙona kansu da kansu- lamarin da ya ƙara dagula halin tsaro a wannan yanki. A cikin wata sanarwa da ta fitar ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce ya zamo wajibi China ta kare haƙƙin addini da yari da kuma al'adun al'umar Tibet . A ranar Litinin 26.09.2011 ne limaman na addinin Budha suka cunna wa kansu wuta domin nuna rashin amincewa da kasancewar wannan yanki a ƙarƙashin ikon China. Gwamnatin Amirka ta kuma buƙaci China da ta ba wa 'yan jarida da wakilan ƙasa da ƙasa ikon sa ido akan halin da ke wakana a lardin Sichuan inda aka gudanar da zanga-zanga a baya-bayan nan. Chinan dai ta gargagɗi Amirka da ta daina yi mata shisshigi a harkokinta na cikin gida.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi