1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirkawa sun fusata da kisan bakar fata

Ramatu Garba Baba
January 29, 2023

Amirka ta dauki mataki na rusa rundunar 'yan sanda da ake wa lakabi da Scorpion bayan da aka samu wasu jami'anta da laifin hannu a kisan wani matashi bakar fata.

https://p.dw.com/p/4Mpua
Zanga-zanga kan kisan Tyre Nichols
Zanga-zanga kan kisan Tyre NicholsHoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Bayan matsi daga masu zanga-zanga, daga bisani mahukuntan Amirka sun sanar da rusa rundunar 'yan sanda ta Memphis a sakamakon rawar da wasu daga cikin jami'anta suka taka a kisan wani matashi bakar fata. Matakin ya biyo bayan sallamar jami'an rundunar biyar da hoton bidiyo ya nunar da yadda suka aikata kisan Tyre Nichols. Duka jami'an da aka sallama sun kasashen bakar fata ne, lamarin da ya zo da mamaki ganin, ba wani sabon abu bane, batun cin zarafin da 'yan sanda farar fata ke yi wa bakaken fata a kasar.

Yaduwar bidiyon yadda jami'an na rundunar da ake wa lakabi da Scorpion suka azabtar da Nicholas kafin su hallaka shi a farkon wannan watan na Janairu, ya matukar fusata Amirkawa, inda suka yi ta gudanar da zanga-zanga, suna kira da a rusa rundunar da aka kafa a watan Nuwambar 2021. Tyre Nichols na da shekaru ashirin da tara a duniya ya kuma mutu ya bar yaro guda mai shekaru hudu da haihuwa da kuma mahaifiyarsa.