1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta sa yaki da ta'addanci kan gaba-gaba

January 21, 2015

A jawabin da shugaba Barack Obama ya gabatar na shekara a yammacin jiya Talata, shugaban ya bayyana cewa tattalin arzikin Amirka na ci gaba da samun tagomashi.

https://p.dw.com/p/1ENas
Barack Obama / Rede zur Lage der Nation / USA
Hoto: Reuters

Shugaba Obama ya ce kuma an samu ci gaban samarwa al'umma ayyukan yi wanda ba a ga irinsa ba a 'yan shekarunnan tun bayan shekarar 1999.

Jawaban shugaban dai sun mai da hankali ne kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki da ilimi da lafiya da samar da ayyukan yi da ababan more rayuwa da kuma huldodin kasuwanci.

Da yake jawabi ga 'yan majalisar kasar ta Amirka wacce ke da rinjayen jam'iyyar Republican ya bukaci a samar da shirin karbar haraji mai sauki da zai tallafi iyalai da suka sadaukar da rayuwarsu wajen bautawa kasa.

Da ya juya kan harkokin kasa da kasa shugaba Obama ya bayyana cewa abu na farko da zai bawa fifiko na zama yaki da ta'addanci inda ya bukaci 'yan majalisar su fitar da matsaya da za ta bada dama wajen amfani da karfin soji wajen murkushe mayakan IS a Siriya da Iraki. Ya kuma bukaci tsaurara matakan tsaro ga harkokin kafar sadarwar intanet da kokarin kasashe wajen yaki da sauyin yanayi.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu