1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta tura dakarunta Sadiyya

Abdul-raheem Hassan
July 20, 2019

Ma'aikatar tsaron kasar Saudiyya ta amince da karbar dakarun Amirka domin inganta matakan tsaro a yankin Gabas ta tsakiya yayin da ake ta kai ruwa rana da kasar Iran.

https://p.dw.com/p/3MMwT
US Truppen im Persischen Golf
Hoto: Imago/ZUMA Press/USMC/Cpl. D. Morgan

Sarki Salman na Saudiyya ya ce matakin ya biyo bayan fahimtar juna tsakanin kasashen biyu domin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta tsakiya.

Rahotanni sun nuna cewa tun kafin Iran ta fara takun saka da Birtaniya kan kwace jiragen dakon man Birtaniya Amirka ta aike da tawagar dakarunta zwua Saudiyya, amma ma'aikatar tsaro ta Pentagon ba ta tabbatar da matakin a hukumance ba sai a baya-bayannan. Tun a shekarar 2013 ne rabon Amirka da tura sojoji Saudiyya bayan janyewar dakarun loakcin da aka gama yakin yakin kasar Iraki.