1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Chaina ta zargi Amirka da cutar mata da 'yan sama jannati

December 28, 2021

Chainan ta ce sai da jami'anta suka yi amfani da dabaru wurin kauce wa wannan babbar barazana da ta faru da su a  watannin Yuli da Oktoba na wannan shekara mai karewa.  

https://p.dw.com/p/44vzB
BdTD China Außenbordeinsatz Raumstation Tianhe
Hoto: Guo Zhongzheng/Xinhua/imago images

Ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta sanar a wannan Talata cewa Amirka ta yi watsi da ka'idojin sararin samaniya, lamarin da ya jefa mata 'yan sama jannati cikin hatsari. Hukumomin Chaina sun shaidawa MDD cewa saura kiris tawagar 'yan sama jannatinta ta yi karo da ta wani kamfani na Amirka.


Kamfanin da Chainan ke zargi da kawo wa tasharta ta 'yan sama jannatin cikas mallakin 'yan kasuwa ne a Amirka. Sai dai hukumomin Beijing sun ce a bisa dokar sararin samaniya kasashe ne ke daukar alhakin abin da kamfanoni suka aikata.