1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta tallafa wa kasashen Afirka

Ahmed Salisu
August 3, 2017

Hukumar nan ta Amirka ta USAID da ke bada agaji a duniya ta ce Shugaba Donald Trump ya amince a fidda dala miliyan 169 don tallafawa wadanda ke fama da ja'ibar yunwa a kasashen da suka hada da Habasha da Kenya.

https://p.dw.com/p/2hezD
Malawi World Food Programme
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb/J. Hrusa

Wata sanarwa da hukumar ta fidda dazu ta ce za a yi amfani da dala miliyan 137 don bada tallafi a Habasha yayin da za a aike da dala miliyan 33 zuwa ga kasar Kenya don tallafa wadanda ke cikin yanayi na bukata. Wannan dai na zuwa ne bayan da watan da ya gabata Shugaba Trump din ya yi alkawarin bada tallafi na kayan abinci da kimarsu ta kai dala miliyan 639 ga kasashe irinsu Somaliya da Sudan ta Kudu da Tarayyar Najeriya da kuma Yemen wadanda wasu bangarorinsu ke fama da rikici.