1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty: Soji na cin zarafin mata a Tigray

Mouhamadou Awal Balarabe
August 11, 2021

Cikin wani sabon rahoton da ta fitar, kungiyar Amnesty International da ke kare hakkin bil Adama ta zargi sojojin Habasha da na Iritirya da yi wa daruruwan mata da 'yan mata fyade a yankin da ake gwabza fada na Tigray.

https://p.dw.com/p/3yph1
Äthiopien | Mai Aini Flüchtlingscamp
Hoto: EDUARDO SOTERAS/AFP/Getty Images

kungiyar Amnesty International da ta himmatu wajen kare hakkin bil Adama a duniya ta ce an ci zarafin wasu daga cikin matan Habasha da Iritiriya ne a lokacin da ake tsare da su. Wannan rahoton da aka wallafa bayan hira da mutane 63 da abin ya rutsa da su, ya zayyana cin zarafin da hukumomin Habasha suka fara bincike a kai, wadanda suka kai ga samun akalla sojoji uku da laifin yin wa mata 25 fyade. Amnesty International ta ce wasu daga cikin matan, an yi musu fyaden ne a gaban ‘yan uwansu.        

Tun a watan Nuwamba ne fada ya fara a yankin Tigray da ke arewancin Habasha  bayan da Firaminista Abiy Ahmed ya tura sojojin don korar hukumomin yankin daga mulki. Shi dai wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2019, ya danganta matakin da mayar da martani na hare -haren da mayakan TPLF suka kai kan sansanin sojojin gwamnatin tarayya.

Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewa kusan mutane 400,000 na rayuwa cikin yanayin 'yunwa a Tigray yanzu haka, yayin da ake samun matsala wajen jigilar agajin jin kai a yankin.