Amnesty ta yi kiran da a janye hukuncin kisa a Edo
October 20, 2012Ƙungiyar dai ta ce ta yi wannan kiran ne saboda a cewarta yankewa mutanen hukuncin kisa wani babban karen tsaye ne ga 'yancinsu na mutuntaka kasancewar a halin yanzu mutanen sun ɗaukaka ƙara game da wannan hukuncin da aka yanke musu.
Da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, kwamishin shari'ar jihar ta Edo Osagie Obayuwana ya ce mutanen da aka yankewa hukuncin sun ɗaukaka ƙara ne bayan lokacin da aka ɗeba musu na ɗaukaka ƙarar ya ƙare, a saboda haka yanzu kam bakin alƙalami ya bushe domin mako biyun da su ka gaba gwamnan jihar Adams Oshiomole ya sanya hannu kan takardar bada umarnin kashe mutanen.
To sai dai duk da wannan bayanai, Amnesty ɗin ta bakin muƙaddashiyar daraktan hukumar ta Afrika Lucy Freeman ta ce matakin da mahukuntan su ka ɗauka ya saɓawa 'yanci na rayuwa da kowanne bil adama ke da shi.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar