1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amsoshi: Tarihin Desmond Tutu

Suleiman Babayo AH
November 15, 2021

Desmond Tutu na raye, kuma jagoran neman adalcin ne na Afirka ta Kudu ya cika shekara 90 a ranar bakwai ga watan Oktoban 2021. Shi ne ya kasance babban limamin darikar Angilika na farko bakar fata.

https://p.dw.com/p/430hX
Südafrika Desmond Tutu
Hoto: Phil Cole/Getty Images

Desmond Tutu shi ne Bischof din Angalika bakar fata na farko a Johannesburg, sannan ya taba zama Archbishop a Cape Town. Ya yi fafutuka tare da Mandela kan wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. An haife shi ne a shekarar ta 1931, a  Transvaal da ke a Afirka  ta Kudu. Desmond Tutu ya fara kama aikin malanta kamar mahaifinsa, amma daga bisani ya dakatar a lokacin da aka bullo da dokar tafiyar da ilimi da aka yi wa laƙabi da “Bantu Education Act” a shekarar 1953. Don haka ne sai ya shiga aikin bushara a majami'u, a inda ya sami matukar goyon baya daga Turawan musamman ma daga Bishop Trevor Huddleston, sakamakon yadda ya nuna kiyayya ga wariyar launin fata.

Desmond Tutu limamin darikar Angilika na farko

Südafrika Desmond Tutu und Nelson Mandela
Hoto: David Brauchli/AP Photo/picture alliance

Desmond Tutu shi ne ya kasance babban limamin darikar Angilika na farko bakar fata a birnin Johannesburg a shekarar ta 1975. Bayan shekara guda da kasancewa a wannan matsayi ne sai shugabannin Turawa fararen fata suka soma sa masa ido saboda irin kyamar da yake ga wariyar launin fata, don haka ne ma ya zamanto mai fafutikar yaki da mulkin wariyar launin fata. A lokacin da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela ke zaman fursuna, Archbishop Desmond Tutu ne ya zamanto babban mai rike wuya ga ‘yan mulkin wariya, don haka ne ma ya sami wata lambar yabo a shekarar 1984, sakamakon wannan gwagwarmaya tasa.

Domin jin krin bayyani mun tanadar muku da sautin a kasa.