1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amsoshin Takardu: dalilin rikicin Kamaru

Salissou Boukari MAB
October 8, 2018

Takaitaccen tarihin yadda kasar Kamaru ta mari yankunan Faransanci da na Ingilishi da kuma tushen wannan rikicin aware da ake fuskanta a daya daga cikin yankunan kasar.

https://p.dw.com/p/36BJH
Karte Kamerun Mamfe Bamenda Buea ENG

Kamaru ta kasance kasar Afirka daya tilo da ta samu 'yancin kai so biyu daga Turawan mulkin mallaka. Bangaren Faransanci ya samun 'yancin kai daga Faransa a ranar 1 ga watan Janairun 1960, yayin da bangaren Ingilishi ya samu 'yancin kai daga Ingila a ranar 1 ga watan Oktan 1961 bayan kada kuri'ar raba gardama.

Honorable Mutari Hamisu, malamin makaranta kuma dan siyasa a yankin Buea da ke Kudu maso yammacin kasar Kamaru ya yi bayani kan dalilan da suka sa kasar ke da yankuna biyu na Ingilishi da kuma na Faransanci, da kuma dalilin rikicin da ya kunno kai yankin Ingilishi.