1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka za ta kakaba wa Iran takunkumi saboda harin Isra'ila

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 16, 2024

Shugabar hukumar kula da baitulmalin Amurka Janet Yellen, ta ce suna tattaunawa da kawayensu don sanin irin takunkumin da ya dace sun sanya wa Iran da zai rage mata karsashi matuka

https://p.dw.com/p/4eqxJ
Hoto: DW

Amurka na shirin kakaba wani sabon takunkumin karya tattalin arziki ga kasar Iran, a matsayin martani ga harin da ta kai wa Isra'ila a baya bayan nan.

Karin bayani:Amurka ta ce babu yaki tsakaninta da Iran

Shugabar hukumar kula da baitulmalin Amurka Janet Yellen, ta ce suna tattaunawa da kawayensu don sanin irin takunkumin da ya dace sun sanya wa Iran da zai rage mata karsashi matuka.

Karin bayani:Kasashen duniya sun caccaki Iran bayan harin Isra'ila

Ta kara da cewa harin na Iran ga Isra'ila wani yunkuri ne na kara dagula zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya, tare da haddasa fantsamar tashin hankalin da yankin ke fama da shi.