1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka za ta kara tallafi a yaki da Ebola

September 9, 2014

Annobar Ebola da tunkarar mayakan sakai daga kungiyar IS batutuwa ne da sai an musu taron dangi a cewar shugaba Obama da Ban Ki-moon.

https://p.dw.com/p/1D96T
UN USA Barak Obama und Ban Ki Moon in New York
Hoto: AP

Shugaba Barack Obama ya bayyana cewa akwai bukatar Amirka ta kara tallafin da take bayarwa dan kawo karshen annobar Ebola a yammacin Afrika.

Fadar ta White House ta ce shugaba Obama ya gabatar da wannnan bukatane a wata hira da ya yi ta wayar tarho da Sakataren MDD Ban Ki-moon a ranar Litinin .

Obama tun da fari ya ce matsalar wannan annoba mai saurin kisa ta Ebola matsala ce da Amirka za ta bawa fifiko, sannan sojan na Amirka za su taimaka wajen samar da kebattattun cibiyoyi da kayan aiki a yammacin na Afrika gami da kulawa da tsaron lafiyar maaikatan jiyyar.

Har ila yau dukkanin shugabanin biyu sun amince cewa barazanar da ake fiskanta daga bangaren mayakan sakai na IS barazana ce da ke bukatar a yi mata taron dangi, sannan a hada kai wajen bada tallafi ga fararen hula da ke fiskantar barazanar dakarun na IS.

Shugabanin kuma sun tattauna kan batun sanya idanu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Ukraine sannan suka duba batutuwa da ake son cimmawa a babban taron MDD da ke tafe.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu