1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da gwamnatin hadin kan Libiya

Gazali Abdou TasawaDecember 24, 2015

Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana goyan bayansa ga yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a Libiya wacce aka cimma a ranar 17 ga watan Disemba.

https://p.dw.com/p/1HSey
Libyen Proteste Februar 2014
Hoto: picture-alliance/dpa

Tuni dai kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniyar ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafa wa sabuwar gwamnatin kasar ta Libiya wacce za ta tare a birnin Tripoli domin ganin ta iya maido da zaman lafiya a kasar musamman ma kawar da Kungiyar IS da ta soma tarewa a kasar.

Sai dai jakadan Faransa a MDD Francois Delattre ya ce sun san cewa sabuwar gwamnatin za ta fuskanci kalubale daga duk masu son yin kafar angulu ga shirin zaman lafiyar. Amma suna kira garesu da su zo su bada hadin kansu tun da sauran lokaci ,kuma su sani idan har za su ci gaba da nacewa kan aniyarsu ta yi wa shirin sabiya to kuwa kwamitin sulhu zai dauki matakan da suka dace kansu.