1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bayyana ƙauyen Bili´in da zama nasara adawa da katangar Isra´ila

September 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuCN

Mazauna kauyen Bili´in dake Gabar yamma da Kogin Jordan sun yi maraba da hukuncin da kotun kolin Isra´ila ta yanke wanda ya umraci Isra´ila da ta canza hanyar ganuwar nan da take ginawa a wannan yanki. Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta saurari karar da Falasdinawa suka shigar cewa katangar ta ratsa kan gonakin su kuma hakan zai zasu shiga cikin halin ni ´yasu. Jim kadan bayan sanar da hukuncin kotun mazauna kauye sun bazu kan tituna suna nuna farin cikin su.

Masharhanta sun bayyana kauyen na Bili´in da cewa wata alamar nasara ce ga adawar da Falasdinawa ke nunawa gina ganuwar.