1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jarida 141 suka mutu a bana

December 19, 2012

Ƙungiyar kula da kare yancin yan jarida wato Repoters Without Borders tace a bana yan jarida da yawa suka mutu

https://p.dw.com/p/175Qd

Kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa wato Reporters without Borders ta fid da rahotonta na shekara-shekara wanda a ciki ta bayyanar da mutuwar 'yan jarida 14 1 wadanda 88 daga cikinsu suka gamu da ajalinsu a lokacin da suke gudanar da aikinsu.

Asarar rayukan 'yan jarida irinta mafi muni tun 1995

Ulrike Gruska, kakakin kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa ta Reporters without borders ta ce:

"Tun daga shekarar 1995 ba a taba samun yawan adadin yan jarida da suka mutu ba kamar a wannan shekara ta 2012 "

Su dai 'yan jaridar guda 88 sun gamu da ajalinsu ne walau a lokacin da suke ba da rahotannin ashin bama -bamai a filin daga ko kuma kisan da masu fataucin miyagun kwayoyi da mayaka 'yan kishin islama ko kuma azzaluman jamiai suka shirya a yi musu.

Mutuwar 'yan jarida lokacin rikici

bA farko wannan wata na Disamba an harbe dan jaridar kasar Masar, Al Hussein Abu Deif a lokacin da rikici ya barke a birnin Alkahira. Shi dai wannan dan jarida mai daukar hoto mai shekaru 33 da ke aiki da jaridar alFajr ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya kutsa fadar shugaba domin daukar hotuna na arangamar da ake yi tsakanin magoya bayan shugaba Mursi da masu adawa da shi. Wani da ya shedar wa idanunsa yadda lamarin ya kasance ya ce wani mutun da ba a san ko shi wa nene ba ya harbe Al Hussein Abu Deif daga kurkusa. Ya kuma mutu ne kwanaki shida bayan da aka harbe shi. A hakika masu ba da rahotannin akan al'uma walau ta hanyar bbog ko kuma kafafen yada labaru sun dandadi kudarsu a wannan shekara ta 2012 Siriya. 'Yan jarida biyar ne dai suka rasa rayukansu a bara. To amma sai gashi yanzu adadin ya karu zuwa 47 a fadin duniya inda a kasar Siriya kadai aka samu mutuwar 44 daga cikinsu.

Christian Estrosi (C), President of Nice Cote D'Azur region and UMP party member, is surrounded by journalists in front of the UMP headquarters as they wait for the result for the new leader of the UMP political party in Paris November 19, 2012. France's UMP party members voted yesterday to select its leader between current secretary-general Jean-Francois Cope and former prime minister Francois Fillon, both of whom have claimed victory in a close election for the UMP party leadership. REUTERS Charles Platiau (FRANCE - Tags: POLITICS)
Hoto: REUTERS

"A dai kasar ta Siriya an samu mutane da suka yi kokarin take haramcin da gwamnatin ta dora akan yada labaru. Su dai wadannan mutane suna amfani ne da wayoyin salula ko kuma hanyar blog wajen ba da labarin abin da ke aukuwa a kasar. Kuma daga gare su ne muke samun labarin abin da ke faruwa a Siriya a nan Jamus, saboda cewa ana rashin kwararrun 'yan jarida da za su iya yin hakan a can kasar." inji Ulrike Gruska kakakin kungiyar 'yan jarida ta Repoters without borders.

A dangane da haka ne ma kungiyar Reporters without Borders ta yi ma wani labari da ta wallafa akan kasar Siriya da ke fama da yaki kai kamar haka "Kushewar 'yan jarida". Ga kuma yadda Nils Metzger da ke aiki da mujallar Zenith ya kwatanta halin da 'yan jarida ke tsintar kansu a ciki a kasar ta Siriya.

Members of French media watchdog Reporters Without Borders gather near the Iranian embassy in Paris, during a demonstration for press freedom in Iran, Thursday June 18, 2009 in Paris. Two riot policemen are seen standing guard rear center. (ddp images/AP Photo/Francois Mori)
Jami'an kungiyar kare yancin yan jarida ta Reporters Without Borders.Hoto: dapd

" Matsalar da abokan aikinmu da ke Siriya ke fuskanta ita ce shiga da suke yi filin daga. Yan tawaye suna korafin cewa ma'aikatan gidajen telebijan na gwamnati ba su yi musu adalci. Dalili kenan da ya sa ake yawaita kai musu hare-hare ake kuma sace su. A ma 'yan watannin da suka shude kungiyoyin 'yan kishin Islama sun kai hare hare da dama akan kafafen yada labaru mallakar gwamnati a Siriya. Haka ma lamarin yake ga abokan aiki da ke wa kafafen yada labarun Rasha aiki. An kuma fuskanci sace-sacen mutane da dama."

An kuma tsare yan jarida da dama

'Yan Jarida 18 ne kuma suka rasa rayukansu a kasar Somaliya awannan shekara. A kasar Pakistan an kashe 'yan jarida goma .Hakazalika 'yan jarida a kasar Mexoíco na cikin hali na tsaka mai wuya a sakamakon rahotannin da suke bayarwa game da masu safarar miyagun kwayoyi . 'Yan jarida shida ne dai suka rasa rayukansu a wannan kasa a wannan shekarar.

Kungiyar Repoters without borders ta kara da cewa akwai kuma 'yan jarida sama da 100o da aka kame a wannan shekarar, a baya ga wasu su dubu biyu da suka fuskanci barazanar kisa ko kuma kai musu hari .

Za a iya sauraron sautin wannan daga kasa.

Mawallafa: Hendrik Heinze/Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu