1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bayyana wanda ya lashe kyautar Nobel

October 11, 2013

Kungiyar dake fafutukar hana amfani da makamai masu guba a lokutan yaki, ta lashe kyautar zaman lafiya ta duniya wato "Nobel Peace Price"

https://p.dw.com/p/19yAJ
OPCW Nihad Alihodzic u.a.Hoto: Reuters

Kungiyar dake rajin hana amfani da makamai masu guba a kan fararen hula a lokutan yaki, da Majalisar Dinkin Duniya ta dorawa alhakin lalata makamai masu guba da Siriya ta mallaka, ta lashe kyautar zaman lafiya ta duniya ta Nobel.

Kungiyar dai ta gudanar da bincike kan zargin da ake yi, na amfani da makamai masu guba a yakin basasar kasar Siriya da yaki ci yaki cinyewa, wanda kuma ya hallaka mutane dubu daya da 400 a watan Agustan da ya gabata.

Daga bisani Majalisar Dinkin Duniya ta dora wa kungiyar alhakin lalata makaman da Siriyan ta mallaka masu guba, wanda hakan ya taimaka wajen dakile yunkurin da Amirka da kawayenta keyi na kai farmakin Soji a kasar.

A yanzu haka dai kimanin kwararrun jami'an wannan kungiya tare da wasu jami'an Majalisar Dinkin Duniya 30 ne a kasar ta Siriya, inda suka fara gudanar da aikin lalata makamai masu guba da Siriyan ta mallaka a karkashin tanade-tanaden kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da aka cimma a karshen watan satumban da ya gabata.

Kwamitin dake zabar wanda ya kamata ya lashe kyautar zaman lafiyar ta duniya, yace ya zabi kungiyar ne bisa kokarin da tayi wajen shiga Siriya domin gudanar da bincike duk kuwa da yakin da ake fafatawa a kasar, wanda hakan ya kawo karshen barazanar daukar matakan soji da Amirka da danginta ke yi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourrahamane Hassane