1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An bude hanyar sufuri a tsakanin Isra'ila da UAE

Ramatu Garba Baba
November 26, 2020

A karon farko bayan sabunta dangantaka a tsakanin juna, jirgin fasinjan Hadaddiyar Daular Larabawa na Flydubai ya soma jigilar fasinjoji daga Isra'ila zuwa birnin Dubai a wannan Alhamis.

https://p.dw.com/p/3lt0M
Israel Corona-Pandemie | Ben Gurion international airport
Hoto: Gil Cohen Magen/Xinhua/imago images

Jama'a da dama sun yi dandanzo a filin jirgin sama a yayin saukar jirgin, fasinjojin cikin yanayi na farin ciki suka yi ta gaisawa da jama'a, wasunsu na nuna alamar nan ta zaman lafiya da yatsunsu. Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya gana da fasinjojin farko da jirgin ya soma kai wa Isra'ilan, yayi musu tarba ta musanman da gaisuwa irin na Islama. A jawabinsa ya baiyana al'amarin da wani kyakyawan babi da zai shiga kundin tarihin duniya.

A watan Satumbar da ya gabata, Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da Amirka ta shiga tsakani, kafin Bharain da Sudan su biyo baya, kasashen Larabawa dai, na ganin za su samu damarmaki na cinikayya da Isra'ilan da aka dade ana gaba da ita amma akwai masu baiyana shakku kan dangantakar.