1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke tsohon Shugaban mulkin Soja na Kasar Pakistan

April 25, 2013

Tsohon Shugaban mulkin Soja na Kasar Pakistan Pervez Musharraf ya shiga hannun Hukuma bisa zarginsa da Kashe tsohuwar Firayim Ministan Kasar Benezir Bhutu

https://p.dw.com/p/18NTo
Pakistan's former President Pervez Musharraf speaks during an interview with Reuters in Dubai March 23, 2013. Musharraf said on Saturday he has been granted bail in advance to avoid being arrested upon his planned return home on Sunday following nearly four years of self-imposed exile. To match Interview PAKISTAN-MUSHARRAF/ELECTIONS REUTERS/Mohammad Abu Omar (UNITED ARAB EMIRATES - Tags: POLITICS)
Pervez Musharraf Rückkehr aus dem ExilHoto: REUTERS

An cafke tsohon Shugaban mulkin Soja na Kasar Pakistan Pervez Musharraf bisa zarginsa da Kasahe tsohuwar Firayim Ministan Kasar Benezir Bhutu.

Masu gabatar da kara sunce kisan Bhutu shine na biyu daga cikin laifuka uku da ake tuhumar sa da aikatawa a yayin da yake kan karagar mulki daga Shekara ta 1999 zuwa 2008.

An dai kama tsohon Shugaba Musaharraf ne kwana guda bayan da wata kotu A pakistan taki amincewa ta kara bada belinshi.

Kame Musharraf da kuma kin amincewa da ya tsaya takarar shugabancin Kasar a zaben da za'a gudanar ranar 11 ga watan mayu mai zuwa ya zamo wani babban kalubale ga tsohon shugaban da ya dawo Pakistan a watan daya gabata yana mai alwashin cewa ya dawo ne domin ya ceto kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu